Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Hosiya 10:1 - Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Isra’ila kuringa ce mai yaɗuwa; ya fitar da ’ya’ya wa kansa. Yayinda ’ya’yan suka ƙaru, ya gina ƙarin bagadai; da ƙasarsa ta wadata, ya yi wa keɓaɓɓun duwatsu ado.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

1 Isra'ila kurangar inabi ce mai bansha'awa Wadda yake ba da 'ya'ya da yawa. Ƙara yawan arzikinsu, Ƙara gina bagadansu. Ƙara yawan wadatar ƙasarsu. Ƙara kyautata ginshiƙansu.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Hosiya 10:1
24 Iomraidhean Croise  

Sun kuma kafa wa kansu masujadai da suke kan tuddai, da a kan keɓaɓɓun duwatsu, suka kuma gina ginshiƙan Ashera a kowane tudu, da kuma a ƙarƙashin kowane duhuwar itace.


Kuna da alloli masu yawa yadda kuke da garuruwa, ya Yahuda; kuma bagadan da kuka yi don ƙona turare wa allahn nan Ba’al abin kunya sun yi yawa kamar titunan Urushalima.’


Ubangiji Maɗaukaki, wanda ya dasa ki, ya furta miki masifa, domin gidan Isra’ila da kuma gidan Yahuda sun aikata mugunta suka kuma tsokane ni in yi fushi ta wurin ƙona wa Ba’al turare.


To ina allolin da kuka yi wa kanku? Bari su zo in suna iya cetonku sa’ad da kuke cikin wahala! Gama kuna da alloli masu yawa kamar yadda kuke da garuruwa, ya Yahuda.


Gileyad mugu ne? Mutanensa mutanen banza ne! Suna miƙa bijimai a Gilgal? Bagadansu za su zama tsibin duwatsu. A gonar da aka nome.


Efraim yana fariya yana cewa, “Ni mai arziki ne ƙwarai; na azurta. Da dukan wadatata ba za a sami wani laifi ko zunubi a gare ni ba.”


ko da ma ya ci gaba cikin ’yan’uwansa. Iskar gabas daga Ubangiji za tă zo, tana hurawa daga hamada; maɓulɓularsa za tă kafe rijiyarsa kuma ta bushe. Za a kwashi kaya masu daraja na ɗakin ajiyarsa ganima.


Yanzu sai yin zunubi a kai a kai suke; suna yin gumaka wa kansu daga azurfansu, da wayo suna sarrafa siffofi, dukansu aikin masu aikin hannu ne. Ana magana waɗannan mutane cewa, “Suna miƙa hadayar mutum su kuma sumbaci gumakan maruƙa.”


Sa’ad da na ciyar da su sun ƙoshi; sa’ad da suka ƙoshi, sai suka fara taƙama; sai suka manta da ni.


Saboda haka yanzu zan buɗe tsiraicinta a idanun kwartayenta; ba wani da zai ƙwace ta daga hannuwana.


Ba ta yarda cewa ni ne wanda ya ba ta hatsi, sabon ruwan inabi da mai ba, wanda ya jibge mata azurfa da zinariya, waɗanda suka yi amfani wa Ba’al ba.


Gama Isra’ilawa za su yi kwanaki masu yawa ba tare da sarki ko shugaba ba, babu hadaya ko keɓaɓɓun duwatsu, babu efod ko gunki.


Yawan ƙaruwar firistoci, haka suke yawan zunubi a kaina; sun yi musaya Ɗaukakarsu da wani abin kunya.


“Ko da yake Efraim ya gina bagadai masu yawa don hadayun zunubi, waɗannan sun zama bagade don yin zunubi.


Suna naɗa sarakuna, ba da izinina ba; sun zaɓa shugabanni ba da yardanta ba. Da azurfa da zinariya sun ƙera gumaka wa kansu wanda zai kai zuwa ga hallakarsu.


“ ‘Kada ku yi gumaka, ko ku kafa siffa, ko al’amudi wa kanku, kada kuma ku sa sassaƙaƙƙun duwatsu a ƙasarku don ku rusuna musu. Ni ne Ubangiji Allahnku.


Ubangiji zai maido da darajar Yaƙub, kamar ta Isra’ila, ko da yake masu washewa sun washe su suka kuma lalatar da inabinsu.


Saboda haka, daga yanzu zuwa nan gaba, ba mu ƙara ɗaukan wani mutum bisa ga ganin duniya ba. Ko da yake a dā, mun ɗauki Kiristi haka, amma yanzu mun daina yin haka.


Gama kowa yana lura da al’amuran kansa ne kawai, ba na Kiristi Yesu ba.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan