Hosiya 1:2 - Sabon Rai Don Kowa 20202 Sa’ad da Ubangiji ya fara magana ta wurin Hosiya, Ubangiji ya ce masa, “Ka tafi, ka auro wa kanka mazinaciya da ’ya’yan da aka haifa ta hanyar rashin aminci, domin ƙasar tana da laifin mummunan zina ta wurin rabuwa da Ubangiji.” Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki2 Sa'ad da Ubangiji ya fara yin magana da Yusha'u ya ce masa, “Tafi ka auro karuwa, ka haifi 'ya'yan karuwanci, gama ƙasar tana yin fasikanci sosai, wato ta bar bin Ubangiji.” Faic an caibideil |
Sa’an nan a cikin al’ummai inda aka kai ku zaman bauta, waɗanda suka a tsere za su tuna da ni, yadda raina ya ɓaci ta wurin zukatansu marasa imani, waɗanda suka rabu da ni, da kuma ta wurin idanunsu, waɗanda suka yi sha’awace-sha’awacen gumakansu. Za su ji ƙyamar kansu saboda mugayen abubuwan da suka aikata.