Sai annabi Haggai, da annabi Zakariya zuriyar Iddo, suka yi wa Yahudawa a Yahuda da Urushalima annabci a cikin sunan Allah na Isra’ila wanda yake da mulki a kansu.
A shekara ta biyu ta mulkin Sarki Dariyus, a rana ta fari ga watan shida, maganar Ubangiji ta zo ta wurin annabi Haggai zuwa ga Zerubbabel ɗan Sheyaltiyel, gwamnan Yahuda, da kuma Yoshuwa ɗan Yehozadak, babban firist.