Daniyel 9:6 - Sabon Rai Don Kowa 20206 Ba mu saurari bayinka annabawa ba, waɗanda suka yi magana a sunanka ga sarakunanmu da masu mulkinmu da iyayenmu, da kuma dukan mutanen ƙasa. Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki6 Ba mu kasa kunne ga bayinka annabawa ba, waɗanda kuwa suka yi magana da sunanka ga sarakunanmu, da shugabanninmu, da kakanninmu, da dukan jama'ar ƙasa. Faic an caibideil |
“To yanzu, ya Allahnmu, mai girma, mai iko, da kuma mai banrazana, wanda yake kiyaye alkawarinsa na ƙauna, kada ka bar dukan wannan wahala ta zama kamar marar muhimmanci a idanunka, wahalar da ta zo a kanmu, a kan sarakunanmu da shugabanni, a kan firistocinmu da annabawa, a kan kakanninmu da kuma dukan mutanenka, daga kwanakin sarakunan Assuriya har yă zuwa yau.