Daniyel 9:4 - Sabon Rai Don Kowa 20204 Na yi addu’a ga Ubangiji Allahna na furta laifina. “Ya Ubangiji, mai alfarma da kuma Allah mai banrazana, wanda yake cika alkawarinsa na ƙauna ga duk wanda ya ƙaunace shi ya kuma kiyaye dokokinsa, Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki4 Na yi addu'a ga Ubangiji Allahna, na tuba. Na ce, “Ya Ubangiji, Allah maigirma, mai banrazana, kai mai cika alkawari ne, kana ƙaunar masu ƙaunarka waɗanda suke kiyaye dokokinka. Faic an caibideil |
“To yanzu, ya Allahnmu, mai girma, mai iko, da kuma mai banrazana, wanda yake kiyaye alkawarinsa na ƙauna, kada ka bar dukan wannan wahala ta zama kamar marar muhimmanci a idanunka, wahalar da ta zo a kanmu, a kan sarakunanmu da shugabanni, a kan firistocinmu da annabawa, a kan kakanninmu da kuma dukan mutanenka, daga kwanakin sarakunan Assuriya har yă zuwa yau.