Daniyel 9:18 - Sabon Rai Don Kowa 202018 Ka kasa kunne, ya Allah, ka kuma ji; ka buɗe idanunka ka kuma ga yadda birninka ya zama kango, birnin da yake ɗauke da Sunanka. Ba cewa muna roƙonka saboda mu masu adalci ba ne, amma saboda girman jinƙanka. Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki18 Ya Allahna, ka karkato kunnenka ka ji, ka buɗe idanunka ka ga yadda mu da birnin da ake kira da sunanka muka lalace. Ba cewa muna da wani adalci na kanmu shi ya sa muka kawo roƙe-roƙenmu ba, amma saboda yawan jinƙanka. Faic an caibideil |