Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 9:10 - Sabon Rai Don Kowa 2020

10 ba mu yi biyayya ga Ubangiji Allahnmu ba, ba mu kuma kiyaye shari’unsa da ya ba mu ta wuri bayinsa annabawa ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

10 Ba mu yi biyayya ga Ubangiji Allahnmu ta wurin kiyaye dokokinsa ba, waɗanda ya ba mu ta hannun bayinsa annabawa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 9:10
8 Iomraidhean Croise  

Wannan ya faru ne domin ba su yi biyayya ga Ubangiji Allahnsu ba, amma suka karya alkawarinsu; da dukan abin da Musa bawan Ubangiji ya umarta. Ba su saurari umarnin ba, balle su kiyaye su.


Sai ka ce musu, ‘Wannan ya zama haka domin kakanninku sun rabu da ni,’ in ji Ubangiji, ‘suka bi waɗansu alloli suka kuma bauta musu. Suka rabu da ni, ba su kuwa kiyaye dokata ba.


Suka shiga suka mallake ta, amma ba su yi maka biyayya ba, ba su kuma bi dokarka ba; ba su yi abin da ka umarce su ba. Saboda haka ka kawo masifa a kansu.


Ba mu saurari bayinka annabawa ba, waɗanda suka yi magana a sunanka ga sarakunanmu da masu mulkinmu da iyayenmu, da kuma dukan mutanen ƙasa.


A dā Allah ya yi wa kakanni-kakanninmu magana ta bakin annabawa a lokuta dabam-dabam da kuma a hanyoyi iri-iri,


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan