Daniyel 8:27 - Sabon Rai Don Kowa 202027 Ni, Daniyel, na gaji matuƙa na kuma yi rashin lafiya na kwanaki masu yawa. Sa’an nan sai na tashi na ci gaba da hidimar sarki. Wahayin ya shige mini duhu, ya fi ƙarfin fahimtata. Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki27 Ni Daniyel kuwa na siƙe, na yi ciwo, har na kwanta 'yan kwanaki, sa'an nan na tashi na ci gaba da aikin sarki. Wahayin ya shige mini duhu, ban gane shi ba. Faic an caibideil |
Sai Daniyel (wanda ake kira Belteshazar) ya tsaya zugum na ɗan lokaci, tunaninsa ya ba shi tsoro. Saboda haka sarki ya ce, “Belteshazar, kada ka bar mafarkin ko ma’anarsa ta tayar maka da hankali.” Belteshazar ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, in dai har mafarkin zai tsaya a kan abokan gābanka da ma’anarsa kuma ta faɗa kan maƙiyan!