Daniyel 8:22 - Sabon Rai Don Kowa 202022 Ƙahoni huɗu da suka maya wannan da ya karye yana a madadin masarautu huɗu da za su tashi daga cikin al’ummarsa amma ba za su sami irin ikonsa ba. Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki22 Ƙahoni huɗu da suka tsiro bayan karyewar na farin, sarakuna huɗu ne da za su fito daga cikin al'ummarsa, amma ba za su sami iko irin nasa ba. Faic an caibideil |
“Bayan haka, a cikin wahayina da dare na duba, a gabana kuwa ga dabba ta huɗu, wadda take da bantsoro da banrazana da kuma iko ƙwarai. Tana da manyan haƙoran ƙarfe; ta ragargaje ta cinye abin da ta kama, ta kuma tattaka duk abin da ya rage a ƙarƙashin ƙafafunta. Ta bambanta da dukan sauran dabbobin da suka riga ta, tana kuma da ƙahoni goma.