Daniyel 8:11 - Sabon Rai Don Kowa 202011 Sai ya ɗora kansa ya zama mai girma kamar Sarkin runduna; sai aka ɗauke hadaya ta kullayaumi daga gare shi, aka kuma saukar da wurin masujadarsa ƙasa. Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki11 Ya ɗaukaka kansa, har ya mai da kansa daidai da shugaban runduna. Ya hana yin hadayar ƙonawa ta yau da kullum ga Sarkin sarakuna, ya kuma rushe masa wuri mai tsarki. Faic an caibideil |
A maimakon, sai ka nuna wa Ubangiji na sama girman kai. Ka sa aka kawo maka su kwaf na zinariya daga haikalinsa, da kai da hakimanka, da matanka da ƙwarƙwaranka kuka sha ruwan inabi da su. Kuka yabi allolin zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba sa ji, ba sa gani, ba sa da gane kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.