Daniyel 7:9 - Sabon Rai Don Kowa 20209 “Ina cikin dubawa, “sai aka ajiye kursiyoyi, sai ga wani wanda yake tun fil azal ya zauna a mazauninsa. Rigarsa ta yi fari fat kamar ƙanƙara; gashin kansa sun yi fari kamar ulu. Kursiyinsa kuma harshen wuta, dukan ƙafafun kursiyin masu kama da keken yaƙin, wuta ne. Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki9 “Ina dubawa sai na ga an ajiye gadajen sarauta, Sai wani wanda yake Tun Fil Azal ya zauna kursiyinsa. Rigarsa fara fat kamar dusar ƙanƙara, Gashin kansa kamar ulu ne tsantsa, Kursiyinsa harshen wuta ne, Ƙafafun kursiyin masu kamar karusa, wuta ne. Faic an caibideil |
Na ga kursiyoyi inda waɗanda aka ba su ikon shari’a suke zama a kai. Sai na ga rayukan waɗanda aka yanke kawunansu saboda shaidarsu don Yesu saboda kuma maganar Allah. Ba su yi wa dabban nan ko siffarta sujada ba, ba su kuma sami alamarta a goshinsu ko a hannuwansu ba. Suka sāke rayuwa daga matattu, suka yi mulki tare da Kiristi shekaru dubu.