Daniyel 7:27 - Sabon Rai Don Kowa 202027 Sa’an nan za a ba da mulki, iko da girma na mulkokin da suke a ƙarƙashin dukan sammai ga tsarkaka, mutane na Mafi Ɗaukaka. Mulkinsa kuwa mulki ne marar matuƙa, kuma dukan masu mulki za su yabe shi, su kuma yi masa biyayya.’ Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki27 Sa'an nan za a ba da sarauta da girman dukan mulkokin duniya ga tsarkaka na Maɗaukaki. Mulkinsa madawwamin mulki ne. Dukan sarakunan duniya za su bauta masa, su kuma yi masa biyayya.’ Faic an caibideil |
Na ga kursiyoyi inda waɗanda aka ba su ikon shari’a suke zama a kai. Sai na ga rayukan waɗanda aka yanke kawunansu saboda shaidarsu don Yesu saboda kuma maganar Allah. Ba su yi wa dabban nan ko siffarta sujada ba, ba su kuma sami alamarta a goshinsu ko a hannuwansu ba. Suka sāke rayuwa daga matattu, suka yi mulki tare da Kiristi shekaru dubu.