Daniyel 7:1 - Sabon Rai Don Kowa 20201 A shekara ta fari ta mulkin Belshazar sarkin Babilon, Daniyel ya yi mafarki, wahayoyi kuma suka ratsa tunaninsa a sa’ad da yake a kwance a gadonsa. Sai ya rubuta abin da mafarkin ya ƙunsa. Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki1 A shekara ta farko ta sarautar Belshazzar Sarkin Babila, Daniyel ya yi mafarki, ya kuma ga wahayi sa'ad da yake kwance a gadonsa. Sai ya rubuta mafarkin. Ga abin da ya faɗa. Faic an caibideil |
“Bayan haka, a cikin wahayina da dare na duba, a gabana kuwa ga dabba ta huɗu, wadda take da bantsoro da banrazana da kuma iko ƙwarai. Tana da manyan haƙoran ƙarfe; ta ragargaje ta cinye abin da ta kama, ta kuma tattaka duk abin da ya rage a ƙarƙashin ƙafafunta. Ta bambanta da dukan sauran dabbobin da suka riga ta, tana kuma da ƙahoni goma.