Daniyel 6:12 - Sabon Rai Don Kowa 202012 Sai suka tafi wurin sarki suka yi masa magana game da dokar mulkinsa, suka ce, “Ashe, ba ka yi doka cewa a cikin kwana talatin nan gaba duk wanda aka tarar yana addu’a ga wani allah ko mutum in ba kai ba, ya sarki, za ka jefa shi a cikin ramin zakoki ba?” Sarki ya amsa ya ce, “Dokar tana nan daram bisa ga dokar Medes da Farisa, waɗanda ba a iya sokewa.” Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki12 Sai suka taho wurin sarki, suka yi magana a kan dokar sarki, suka ce, “Ran sarki ya daɗe! Ashe, ba ka sa hannu a dokar ba, cewa cikin kwana talatin nan gaba kada kowa ya yi addu'a ga wani gunki ko mutum, in ba a gare ka ba, sai a jefa shi a kogon zakoki?” Sai sarki ya amsa, ya ce, “Dokar tabbatacciya ce, gama dokar Mediya da Farisa, ba ta sokuwa.” Faic an caibideil |