Daniyel 5:7 - Sabon Rai Don Kowa 20207 Sai sarki ya kira masu dabo, masanan taurari da masu duba, a kawo su, ya kuma ce wa masu hikima na Babilon, “Duk wanda ya karanta wannan rubutu ya kuma faɗa mini abin da yake nufi, za a sa masa rigar shunayya, a kuma sa masa sarƙar zinariya a wuyansa, zai zama na uku a cikin masu mulkin ƙasar.” Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki7 Sai sarki ya yi kira da babbar murya, cewa a kawo masu dabo, da bokaye, da masu duba. Sai sarki ya ce wa masu hikima na Babila, “Dukan wanda ya karanta wannan rubutu, ya faɗa mini ma'anarsa, to, za a sa masa rigar shunayya, a kuma sa masa sarƙar zinariya a wuyansa, zai zama shi ne na uku a cikin masu mulkin ƙasar.” Faic an caibideil |
Akwai wani mutum a masarautarka wanda yake da ruhun alloli masu tsarki a cikinsa. A zamanin mahaifinka an gane cewa yana da basira da hazaka da hikima kamar na alloli. Sarki Nebukadnezzar mahaifinka, mahaifinka sarki, na ce, ya naɗa shugaban masu dabo, da masu sihiri, masanan taurari da kuma masu duba.