Daniyel 5:3 - Sabon Rai Don Kowa 20203 Sai suka kawo kayan zinariyan nan da aka kwaso daga haikalin Allah a Urushalima, sarki kuwa da hakimansa, da matansa, da ƙwarƙwaransa suka yi ta sha da su. Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki3 Sai suka kawo tasoshin zinariya da na azurfa waɗanda aka kwaso daga cikin Haikali, wato Haikalin Allah a Urushalima. Sai sarki da manyan mutanensa, da matansa, da ƙwaraƙwaransa, suka yi ta sha da su. Faic an caibideil |
A maimakon, sai ka nuna wa Ubangiji na sama girman kai. Ka sa aka kawo maka su kwaf na zinariya daga haikalinsa, da kai da hakimanka, da matanka da ƙwarƙwaranka kuka sha ruwan inabi da su. Kuka yabi allolin zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba sa ji, ba sa gani, ba sa da gane kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.