Daniyel 5:12 - Sabon Rai Don Kowa 202012 Wannan mutum Daniyel, wanda sarki ya kira Belteshazar, an gane yana da ruhu nagari, da ilimi, da ganewa don yin fassarar mafarkai, da bayyana ma’anar kacici-kacici, da warware al’amura masu wuya. Ka kira Daniyel shi kuwa zai faɗa maka abin da rubutun nan yake nufi.” Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki12 Yana da ruhun nagari, da ilimi, da ganewa don yin fassarar mafarkai, da bayyana ma'anar ka-cici-ka-cici, da warware al'amura masu wuya. Shi ne wanda sarki ya laƙaba wa suna Belteshazzar. Don haka sai a kirawo maka Daniyel, shi kuwa zai sanar maka da ma'anar.” Faic an caibideil |
Sai Daniyel (wanda ake kira Belteshazar) ya tsaya zugum na ɗan lokaci, tunaninsa ya ba shi tsoro. Saboda haka sarki ya ce, “Belteshazar, kada ka bar mafarkin ko ma’anarsa ta tayar maka da hankali.” Belteshazar ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, in dai har mafarkin zai tsaya a kan abokan gābanka da ma’anarsa kuma ta faɗa kan maƙiyan!