Daniyel 4:32 - Sabon Rai Don Kowa 202032 Za a kore ka daga cikin mutane za ka kuma yi rayuwa tare da namun jeji. Za ka ci ciyawa kamar sa har shekara bakwai cif, sa’an nan za ka gane Mafi Ɗaukaka ne mai iko duka a kan dukan mulkoki a duniya, yake kuma ba da mulki ga duk wanda ya ga dama.” Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki32 Za a kuma kore ka daga cikin mutane zuwa jeji, ka zauna tare da namomin jeji. Za ka ci ciyawa kamar sa har shekara bakwai cur, sa'an nan za ka gane Maɗaukaki ne yake sarautar 'yan adam, yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama.” Faic an caibideil |
Aka kore shi daga cikin mutane aka kuma ba shi tunani irin na dabba; ya yi zama tare da jakunan jeji, ya kuma ci ciyawa kamar shanu; jikinsa kuma ya jiƙe da raɓa, har zuwa lokacin da ya gane, ashe, Allah Maɗaukaki ne mai iko duka a kan dukan mulkoki a duniya, yake kuma ba da mulki ga duk wanda ya ga dama.