Daniyel 4:1 - Sabon Rai Don Kowa 20201 Daga sarki Nebukadnezzar. Zuwa ga mutane da al’ummai da kuma kowane yare, da suke zama a duniya. Salama mai yawa ta tabbata a gare ku! Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki1 “Daga sarki Nebukadnezzar zuwa ga dukan mutane, da al'ummai, da harsuna mabambanta waɗanda suke zaune a duniya duka. Salama mai yawa ta tabbata a gare ku! Faic an caibideil |
Sa’an nan aka kira magatakardun sarki a rana ta goma sha uku na wata na fari. Suka rubuta dukan umarnin Haman a irin rubutun kowane lardi, kuma cikin harshen kowane mutane, zuwa ga shugabannin mahukuntai na sarki, da gwamnonin larduna dabam-dabam, da kuma hakiman mutane dabam-dabam. Aka rubuta waɗannan a sunan Sarki Zerzes da kansa, aka kuma hatimce da zobensa.
Nan da nan aka kira magatakardun fada, a ranar ashirin da uku ga watan uku, wato, watan Siban. Suka rubuta dukan umarnan Mordekai ga Yahudawa, da kuma ga shugabanni, da gwamnoni, da hakiman larduna 127 tun daga Indiya har zuwa Kush. Aka rubuta waɗannan umarnan a rubutun kowane lardi, da kuma cikin harshen kowane mutane. Aka kuma rubuta ga Yahudawa a rubutunsu da harshensu.