Daniyel 3:7 - Sabon Rai Don Kowa 20207 Saboda haka, da zarar suka ji karar ƙaho, da sarewa, garaya da goge da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe da kowane irin kaɗe-kaɗe kowane mutum da ko wace al’umma da kowane irin yare suka sunkuya suka yi sujada ga wannan siffa ta zinariya da sarki Nebukadnezzar ya kafa. Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki7 Don haka da dukan mutane, da al'ummai, da harsuna mabambanta sun ji ƙarar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo, da algaita, da kowane irin abin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, sai suka fāɗi ƙasa, suka yi sujada ga gunkin zinariya wanda sarki Nebukadnezzar ya kafa. Faic an caibideil |
Dabbar da ka gani, a dā ta taɓa kasancewa, a yanzu, ba ta, za tă kuma fito daga Abis zuwa ga hallakarta. Mazaunan duniya waɗanda ba a rubuta sunayensu a littafin rai tun kafin halittar duniya ba za su yi mamaki sa’ad da suka ga dabbar, domin a dā ta taɓa kasancewa, yanzu kuwa ba ta, duk da haka za tă dawo.