Daniyel 3:1 - Sabon Rai Don Kowa 20201 Sarki Nebukadnezzar ya yi gunkin zinariya, tsawonsa kamu tasa’in, fāɗinsa kuma kamu tara ne, ya kafa shi a filin Dura a yankin Babilon. Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki1 Sarki Nebukadnezzar ya yi gunki na zinariya wanda tsayinsa kamu sittin ne, fāɗinsa kuma kamu shida. Ya kafa shi a filin Dura wanda yake a lardin Babila. Faic an caibideil |
A maimakon, sai ka nuna wa Ubangiji na sama girman kai. Ka sa aka kawo maka su kwaf na zinariya daga haikalinsa, da kai da hakimanka, da matanka da ƙwarƙwaranka kuka sha ruwan inabi da su. Kuka yabi allolin zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba sa ji, ba sa gani, ba sa da gane kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.