Daniyel 2:47 - Sabon Rai Don Kowa 202047 Sarki ya kuma ce wa Daniyel, “Tabbatacce Allahnka shi ne Allahn alloli da kuma Sarkin sarakuna da mai bayyana asirai, gama ka iya bayyana wannan asiri.” Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki47 Ya kuma ce wa Daniyel, “Hakika, Allahnka, Allahn alloli ne da Ubangijin sarakuna, mai bayyana asirai, gama ka iya bayyana wannan asiri.” Faic an caibideil |
Yanzu sa’ad da kuka ji karar ƙaho, da sarewa, da garaya, da goge, da molo da algaita da kowane irin kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, in kuna a shirye ku rusuna ƙasa ku yi wa wannan gunkin da na yi sujada, to, da kyau. Amma in ba ku yi sujada ba, za a je fa ku yanzu a cikin tanderun wutar nan. In ga kowane ne allahn nan da zai kuɓutar da ku daga hannuna?”
Akwai wani mutum a masarautarka wanda yake da ruhun alloli masu tsarki a cikinsa. A zamanin mahaifinka an gane cewa yana da basira da hazaka da hikima kamar na alloli. Sarki Nebukadnezzar mahaifinka, mahaifinka sarki, na ce, ya naɗa shugaban masu dabo, da masu sihiri, masanan taurari da kuma masu duba.