Daniyel 2:45 - Sabon Rai Don Kowa 202045 Wannan shi ne ma’anar wannan wahayin da ka gani na dutsen da aka yanko daga jikin tsaunin, amma ba da hannun ɗan adam ba, dutsen da ya ragargaza ƙarfen, da tagullar, da yumɓun da azurfar da kuma zinariyar. “Allah mai girma ya nuna wa sarki abin da zai faru nan gaba. Mafarkin gaskiya ne, fassararsa kuma abin dogara ne.” Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki45 Kamar yadda ka ga an gutsuro dutse ba da hannun ɗan adam ba, ya kuwa ragargaje baƙin ƙarfen, da tagullar, da yumɓun, da azurfar, da zinariyar, Allah Maɗaukaki ya sanar wa sarki abin da zai faru nan gaba. Mafarkin tabbatacce ne, fassarar kuma gaskiya ce.” Faic an caibideil |
“To yanzu, ya Allahnmu, mai girma, mai iko, da kuma mai banrazana, wanda yake kiyaye alkawarinsa na ƙauna, kada ka bar dukan wannan wahala ta zama kamar marar muhimmanci a idanunka, wahalar da ta zo a kanmu, a kan sarakunanmu da shugabanni, a kan firistocinmu da annabawa, a kan kakanninmu da kuma dukan mutanenka, daga kwanakin sarakunan Assuriya har yă zuwa yau.