Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 2:14 - Sabon Rai Don Kowa 2020

14 Sa’ad da Ariyok, shugaban ƙungiyar matsaran sarki, ya fita domin yă kashe masu hikima na Babilon, sai Daniyel ya yi masa magana cikin hikima da dabara.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

14 Daniyel kuwa ya amsa wa Ariyok, shugaban dogaran sarki, a hankali da hikima, sa'ad da Ariyok ya fita don ya karkashe masu hikima na Babila.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 2:14
8 Iomraidhean Croise  

Ana cikin haka, Midiyawa suka sayar da Yusuf a Masar wa Fotifar, ɗaya daga cikin shugabannin ’yan gadin fadar Fir’auna.


Nebuzaradan shugaban matsaran sarki ya kwashi mutanen da suka rage a birnin zuwa zaman bauta a Babilon, tare da waɗanda suka riga suka tafi wurinsa, da kuma sauran mutanen.


A kan rana ta goma ga watan biyar a shekara ta goma sha tara ta sarautar Nebukadnezzar, Sarkin Babilon, sai Nebuzaradan shugaban matsara da kuma ɗan majalisar sarki, ya zo Urushalima.


Sojojin Babiloniyawa da suke tare da shugaban matsara, suka rushe dukan katangan Urushalima.


Ya tambayi mai tsaro na sarki, “Me ya sa sarki ya fitar da wannan doka haka da fushi?” Sai Ariyok ya yi wa Daniyel bayanin batun.


Sai Daniyel ya tafi wurin Ariyok, wanda sarki ya sa yă kashe masu hikiman Babilon, ya kuma ce masa, “Kada ka kashe masu hikiman Babilon ka kai ni wurin sarki, ni kuma zan fassara masa mafarkinsa.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan