Daniyel 11:6 - Sabon Rai Don Kowa 20206 Bayan ’yan shekaru, za su haɗa kai. Diyar sarkin Kudu za tă je wurin sarkin Arewa ta sada zumunci, amma ba za tă riƙe iko ba, shi kuwa da ikonsa ba za su daɗe ba. A waɗannan kwanaki za a bashe ta, da ita da masu rakiyarta da kuma mahaifinta da kuma wanda ya goyi bayanta. Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki6 Bayan waɗansu shekaru za su ƙulla zumunci. Sarkin kudu zai aurar wa sarkin arewa da 'yarsa don sāda zumunci, amma ba za ta sami iko ba. Shi da zuriyarsa ba za su amince da ita ba. Za a yi watsi da ita, ita da masu yi mata hidima, da mahaifinta, da waliyyinta. Faic an caibideil |