Daniyel 11:12 - Sabon Rai Don Kowa 202012 Sa’ad da zai kawar da rundunar, sarkin Kudu zai cika da girman kai zai kuma kashe mutane dubbai, duk da haka ba zai kasance mai nasara ba. Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki12 Ganin ya kashe sojoji masu ɗumbun yawa, sai ya yi girmankai, amma nasararsa ba mai ɗorewa ba ce. Faic an caibideil |
A maimakon, sai ka nuna wa Ubangiji na sama girman kai. Ka sa aka kawo maka su kwaf na zinariya daga haikalinsa, da kai da hakimanka, da matanka da ƙwarƙwaranka kuka sha ruwan inabi da su. Kuka yabi allolin zinariya da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse waɗanda ba sa ji, ba sa gani, ba sa da gane kome. Amma ba ka girmama Allah ba, wanda ranka da dukan harkokinka suna a hannunsa.