Daniyel 10:16 - Sabon Rai Don Kowa 202016 Sai wani wanda ya yi kama da mutum ya taɓa leɓunana, na kuma buɗe bakina sai na fara magana. Na ce wa wannan da yake tsaye a gabana, “Na cika da azaba saboda wannan wahayi, ranka yă daɗe, ina kuma neman taimako. Faic an caibideilLittafi Mai Tsarki16 Sai wani mai kama da ɗan adam ya taɓa leɓunana, sa'an nan na buɗe baki, na yi magana, na ce wa wanda yake tsaye gabana, “Ya shugabana saboda wannan wahayi ciwo ya kama ni, ba ni da sauran ƙarfi. Faic an caibideil |
Sai Daniyel (wanda ake kira Belteshazar) ya tsaya zugum na ɗan lokaci, tunaninsa ya ba shi tsoro. Saboda haka sarki ya ce, “Belteshazar, kada ka bar mafarkin ko ma’anarsa ta tayar maka da hankali.” Belteshazar ya amsa ya ce, “Ranka yă daɗe, in dai har mafarkin zai tsaya a kan abokan gābanka da ma’anarsa kuma ta faɗa kan maƙiyan!
Gideyon ya ce, “Ranka yă daɗe, in Ubangiji yana tare da mu, me ya sa waɗannan abubuwa suka faru da mu? Ina dukan abubuwan al’ajabinsa waɗanda kakanninmu suka gaya mana game su sa’ad da suka ce, ‘Ashe, ba Ubangiji ne ya fitar da mu daga Masar ba?’ Amma yanzu Ubangiji ya rabu da mu ya kuma sa mu hannun Midiyawa.”