Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 10:11 - Sabon Rai Don Kowa 2020

11 Sai ya ce, “Daniyel, kai ne wanda ake ƙauna sosai, ka yi lura da kyau game da kalmomin da zan yi maka magana a kansu, ka tashi yanzu, gama an aiko ni a gare ka.” Sa’ad da ya faɗa mini haka, sai na tashi a tsaye ina rawan jiki.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

11 Ya ce mini, “Ya Daniyel, mutumin da ake sonka ƙwarai, ka lura da maganar da zan faɗa maka. Ka miƙe tsaye, gama a wurinka aka aiko ni.” Sa'ad da ya faɗi wannan magana, sai na miƙe tsaye, ina rawar jiki.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 10:11
15 Iomraidhean Croise  

“Wannan ya sa gabana ya fāɗi, zuciyata ta yi tsalle.


Sarki ya cika da sha’awar kyanki; ki girmama shi, gama shi ne maigidanki.


Ni ta ƙaunataccena ce, kuma sha’awarsa domina ne.


ko da waɗannan mutum uku Nuhu, Daniyel da kuma Ayuba suna a cikinta, za su iya ceton kansu ne kawai ta wurin adalcinsu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.


Ya ce mini, “Ɗan mutum, tashi ka tsaya a ƙafafunka zan kuma yi maka magana.”


Ya kuma ce, “Kada ka ji tsoro, ya kai mutumin da ake fahariya, salama a gare ka! Ka ƙarfafa yanzu; ka yi ƙarfin hali.” Sa’ad da ya yi magana da ni, sai na samu ƙarfi na ce, “Ka yi magana ranka yă daɗe, tun da yake ka sa na sami ƙarfi.”


Ban ci abinci mai kyau ba; ba nama ko ruwa inabin da ya shiga bakina; kuma ba na amfani da man shafawa gaba ɗaya har sai da sati nan uku suka wuce.


Da rawan jiki da kuma ruɗewa, matan suka fita a guje daga kabarin. Ba su kuwa gaya wa kowa ba, don suna tsoro. [Waɗansu rubuce-rubucen hannu na farko-farko da waɗansu shaidu na dā ba su da ayoyi 9-20.]


Ɗaya daga cikin almajiran Yesu wanda yake ƙauna kuwa, yana zaune kusa da shi.


Bitrus ya juya ya ga cewa almajirin nan da Yesu yake ƙauna yana binsu. (Wannan ne ya jingina a jikin Yesu sa’ad da suke cin abincin yamman nan da ya ce, “Ubangiji wane ne zai bashe ka?”)


Yanzu ka tashi, ka tsaya da ƙafafunka. Na bayyana a gare ka don in naɗa ka bawa da kuma mai shaidar abin da ka gani game da ni da kuma abin da zan nuna maka.


Yanzu ka tashi ka shiga cikin birnin, za a kuma gaya maka abin da dole za ka yi.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan