Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 10:1 - Sabon Rai Don Kowa 2020

1 A shekara ta uku ta Sairus sarkin Farisa, sai aka ba wa Daniyel (wanda ake kira Belteshazar) wahayi. Saƙon kuwa gaskiya ce wadda take tattare da babban yaƙi. Fahimtar saƙon ya zo masa a cikin wahayi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

1 A shekara ta uku ta sarautar Sairus Sarkin Farisa, sai aka aiko da saƙo wurin Daniyel, wanda aka laƙaba wa suna Belteshazzar. Saƙon kuwa gaskiya ne, ya shafi zancen yaƙi, Daniyel kuwa ya fahimci saƙon.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 10:1
28 Iomraidhean Croise  

Dalilin da aka ba wa Fir’auna mafarkan nan kashi biyu kuwa shi ne cewa Allah ya riga ya ƙaddara al’amarin. Allah zai aikata shi, ba da daɗewa ba.


Don a cika maganar da Ubangiji ya yi ta wurin Irmiya, a shekara farko ta Sairus sarkin Farisa, sai Ubangiji ya motsa zuciyar Sairus na Farisa don yă yi shela a dukan masarautarsa, ya kuma sa shi a rubuce cewa,


Sai suka ba wa magina da kafintoci kuɗi, suka ba wa mutanen Sidon da na Taya abinci, da abin sha, da mai, don su kawo itatuwan al’ul a Yaffa daga Lebanon ta teku, yadda Sairus sarkin Farisa ya ba da umarni.


Amma Zerubbabel, Yeshuwa, da sauran shugabannin iyalai na Isra’ila suka amsa suka ce, “Ba za ku sa hannu cikin gina wa Allahnmu haikali ba, mu kaɗai za mu gina wa Ubangiji, Allah na Isra’ila gini kamar yadda Sarki Sairus, sarkin Farisa, ya umarce mu.”


Suka yi hayar mashawarta don su ga cewa sun ɓata ƙoƙarinsu dukan kwanakin mulkin Sairus sarkin Farisa har zuwa kwanakin mulkin Dariyus sarkin Farisa.


Dattawan Yahuda kuwa suka ci gaba da ginin suna yin nasara ta wurin wa’azin Haggai annabi da Zakariya ɗan Iddo. Suka kuma gama ginin haikalin bisa ga umarnin Allah na Isra’ila da kuma umarnin Sairus da Artazerzes, sarakunan Farisa.


A shekara ta farko ta mulkin sarki Sairus, sarki ya ba da umarni game da haikalin Allah a Urushalima, ya ce, Bari a sāke gina haikalin yă zama wurin miƙa hadayu, a kuma aza harsashin ginin haikalin. Tsayinsa zai zama ƙafa tasa’in, fāɗinsa kuma kamu tasa’in.


wanda ya yi zancen Sairus ya ce, ‘Shi ne makiyayina zan kuma cika dukan abin da na gan dama; zai yi zancen Urushalima cewa, “Bari a sāke gina ta,” game da haikali kuma cewa, “Bari a kafa harsashinsa.” ’


Ga samarin nan guda huɗu Allah ya ba su sani da ganewar dukan irin littattafai da kuma koyarwa. Daniyel kuma ya iya gane wahayi da kowane irin mafarki.


Daniyel kuwa ya kasance a nan har shekara ta farko ta mulkin sarki Sairus.


Sai sarkin fada ya raɗa musu sababbin sunaye, ga Daniyel ya raɗa masa Belteshazar; ga Hananiya ya raɗa masa Shadrak; ga Mishayel ya raɗa masa Meshak; ga Azariya kuma ya raɗa masa Abednego.


Yanzu na zo domin in bayyana maka abin da zai faru da mutanenka nan gaba, gama wahayin ya shafi lokacin da bai riga ya zo ba ne.”


“Yanzu dai, zan faɗa maka gaskiya. Sarakuna uku za su taso a Farisa, sa’an nan kuma na huɗu, wanda zai fi dukansu dukiya. Sa’ad da zai sami iko saboda dukiyarsa, zai zuga dukan kowane mutum yă yi gāba da masarautar Girka.


Amma kai, Daniyel, ka rufe zancen nan ka kuma liƙe kalmomin littafin nan har sai ƙarshe. Mutane da yawa za su yi ta kai komo don neman sani.”


Sai ya amsa ya ce, “Ka kama hanyarka, Daniyel, domin a rufe kalmomin aka kuma liƙe su har sai ƙarshen lokaci.


Yana sāke lokuta, yana tuɓe sarakuna yana kuma naɗa waɗansu. Yana ba da hikima ga masu hikima kuma ilimi ga masu basira.


A ƙarshe, sai Daniyel ya zo gabana na kuma faɗa masa mafarkin. (Ana ce da shi Belteshazar, wanda aka ba shi sunan allahna kuma ruhun alloli masu tsarki suna a bisansa.)


Wannan mutum Daniyel, wanda sarki ya kira Belteshazar, an gane yana da ruhu nagari, da ilimi, da ganewa don yin fassarar mafarkai, da bayyana ma’anar kacici-kacici, da warware al’amura masu wuya. Ka kira Daniyel shi kuwa zai faɗa maka abin da rubutun nan yake nufi.”


Sai Daniyel ya amsa wa sarki ya ce, “Za ka iya ajiye kyautar wa kanka ko kuma ka ba wa wani. Duk da haka, zan karanta wa sarki rubutun, in kuma faɗa abin da yake nufi.


Daniyel kuwa ya bunkasa a lokacin mulkin Dariyus da kuma mulkin Sairus na Farisa.


Sai na ji muryar wani mutum daga Ulai tana cewa, “Jibra’ilu, faɗa wa wannan mutum ma’anar wahayin.”


“Wahayin nan na safiya da yamma da aka nuna maka gaskiya ne, amma ka ɓoye wahayin, gama ya shafi nan gaba mai tsawo ne.”


Yanzu za ka zama bebe, ba za ka ƙara iya magana ba sai ranar da wannan magana ta cika, saboda ba ka gaskata da kalmomina waɗanda za su zama gaskiya a daidai lokacinsu ba.”


Sai mala’ikan ya ce mini, “Rubuta, ‘Masu albarka ne waɗanda aka gayyace su zuwa bikin auren Ɗan Ragon!’ ” Sai ya ƙara da cewa, “Waɗannan su ne kalmomin Allah da gaske.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan