Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Daniyel 1:17 - Sabon Rai Don Kowa 2020

17 Ga samarin nan guda huɗu Allah ya ba su sani da ganewar dukan irin littattafai da kuma koyarwa. Daniyel kuma ya iya gane wahayi da kowane irin mafarki.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Littafi Mai Tsarki

17 Waɗannan samari huɗu kuwa, Allah ya ba su ilimi, da sanin littattafai, da hikima. Ya kuma yi wa Daniyel baiwar ganewar wahayi da mafarkai.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Daniyel 1:17
36 Iomraidhean Croise  

zan yi abin da ka roƙa. Zan ba ka zuciya mai hikima da ta ganewa, har yă zama ba a taɓa samun wani kamar ka ba, ba kuwa za a taɓa samunsa ba.


Sa’ad da dukan Isra’ila suka ji hukuncin da sarki ya zartar, suka girmama sarki sosai, domin sun gane cewa Allah ya ba shi hikimar yin shari’ar adalci.


Ka ba ni hikima da sani, don in iya jagorance wannan mutane, gama wa zai iya shugabance wannan jama’arka mai girma?”


saboda haka za a ba ka hikima da sani. Zan kuma ba ka wadata, arziki da girma, waɗanda babu wani sarki kafin kai da ya taɓa kasance da su kuma babu wani a bayanka da zai kasance da su.”


Ya nemi Allah a kwanakin Zakariya, wanda ya koyar da shi a tsoron Allah. Muddin ya nemi Ubangiji, Allah ya ba shi nasara.


Amma ruhun da yake cikin mutum, numfashin Maɗaukaki shi ne yake ba shi ganewa.


Gama Ubangiji yana ba da hikima, daga bakinsa kuma, sani da ganewa sukan fito.


Ga wanda ya gamshe shi, Allah yakan ba da hikima da sani da farin ciki, amma ga mai zunubi yakan ba shi aikin tarawa da ajiyar dukiya domin yă miƙa wa wanda ya gamshi Allah. Wannan ma ba shi da amfani, naushin iska ne kawai.


Allahnsa ya umarce shi ya kuma koya masa hanyar da take daidai.


Ka fi Daniyel hikima ne? Ba asirin da yake ɓoye a gare ka?


A ƙarshen lokacin da sarki ya sa da za a kawo su ciki, sai sarkin fada ya gabatar da su ga Nebukadnezzar.


A dukan al’amuran hikima da na fahimta wanda sarki ya tambaye su, ya tarar sun fi dukan masu sihiri da bokaye waɗanda suke cikin mulkinsa sau goma.


Matasa maza waɗanda ba su da wata naƙasa kuma kyawawa, hazikai ta kowace hanyar koyo, sanannu, masu saurin fahimtar abu, da kuma waɗanda suka cancanci su yi aiki a fadar sarki. Zai koya musu harshen Babiloniyawa da kuma littattafansu.


A shekara ta uku ta Sairus sarkin Farisa, sai aka ba wa Daniyel (wanda ake kira Belteshazar) wahayi. Saƙon kuwa gaskiya ce wadda take tattare da babban yaƙi. Fahimtar saƙon ya zo masa a cikin wahayi.


A wannan dare sai aka bayyana wa Daniyel mafarkin cikin wahayi. Daniyel kuwa ya ɗaukaka Allah na sama.


Yana sāke lokuta, yana tuɓe sarakuna yana kuma naɗa waɗansu. Yana ba da hikima ga masu hikima kuma ilimi ga masu basira.


Na gode maka ina yabonka, Allah na kakannina. Kai ka san hikima da iko, ka sanar da ni abin da muka tambaye ka, ka kuma sanar da mu mafarkin sarki.”


Amma ba a bayyana mini wannan asiri saboda ina da wata hikima fiye da sauran mutane ba, sai dai domin a sanar wa sarki da fassarar, ka kuma san tunanin da ya shiga zuciyarka.


Don haka na ba da umarni a tattaro dukan masu hikima na Babilon su bayyana a gabana domin su fassara mini mafarkin.


Na sami labari cewa kana da ruhun alloli a cikinka da kuma basira, da hazaka da kuma fitacciyar hikima.


A shekara ta fari ta mulkin Belshazar sarkin Babilon, Daniyel ya yi mafarki, wahayoyi kuma suka ratsa tunaninsa a sa’ad da yake a kwance a gadonsa. Sai ya rubuta abin da mafarkin ya ƙunsa.


A shekara ta uku ta mulkin sarki Belshazar, ni, Daniyel, na ga wahayi, bayan wancan da na riga gani.


sai ya ce, “Ku ji abin da zan faɗa, “Duk lokacin da akwai annabin Ubangiji a cikinku, nakan bayyana kaina gare shi cikin wahayi, in yi magana da shi cikin mafarkai.


Gama zan ba ku kalmomi, da hikima waɗanda ba ko ɗaya daga cikin maƙiyanku, za su iya tsayayya da ku, ko su ƙaryata.


amma ba su iya cin nasara kan hikimarsa ko kuma a kan Ruhu wanda ta wurinsa ne ya magana ba.


ya kuma cece shi daga dukan wahalolinsa. Ya ba wa Yusuf hikima ya kuma sa ya sami farin jini a wurin Fir’auna, sarkin Masar; saboda haka ya mai da shi mai mulki a kan Masar da kuma dukan fadarsa.


Musa ya sami ilimi cikin dukan hikimar Masarawa ya kuma zama mai iko cikin magana da ayyuka.


Shi ya sa tun daga ranar da muka sami labarin, ba mu fasa yin addu’a dominku ba. Kullum muna roƙon Allah yă sa ku san kome da yake so ku yi, domin ku sami hikima ta Ruhu, ku kuma sami ganewar kome duka.


Kowane abu mai kyau da kuma kowace cikakkiyar kyauta daga sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.


In waninku ya rasa hikima, ya kamata yă roƙi Allah, mai bayarwa hannu sake ga kowa ba tare da gori ba, za a kuwa ba shi.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan