“Ka sauko a kan Dutsen Sinai; ka yi musu magana daga sama. Ka ba su ƙa’idodi da dokokin da suke masu adalci da kuma daidai, ka ba su farillai da umarnai da suke da kyau.
Kada ku ci gaba da yin abin da duniya take yi, sai dai ku bar halinku ya sāke, ta wurin sabunta hankalinku ɗungum, don ku tabbatar da abin da Allah yake so yake, abu mai kyau, mai daɗi da kuma cikakke.
Gama na san cewa babu wani abin kirkin da yake zaune a cikina, wato, a mutuntakata. Gama sha’awar yin abu mai kyau kam ina da ita, sai dai ikon yin ne fa babu.
To, Dokar ce tana gāba da alkawaran Allah ke nan? Sam, ko kaɗan! Gama da a ce an ba da Dokar da tana iya ba da rai, tabbatacce, da sai a sami adalci ta wurin Doka.