Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Zefaniya 3:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Shugabanninsa zakoki ne masu ruri, Alƙalansa kuma kyarketai ne da sukan fito da maraice, Waɗanda ba su rage kome kafin wayewar gari.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Sarakunanki ruri ne na zakoki, shugabanninki kyarketan dare ne, waɗanda ba sa rage kome don safe.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Zefaniya 3:3
15 Iomraidhean Croise  

Talakawa ba su da wani taimako sa'ad da suke ƙarƙashin mulkin mugun. Abin tsoro ne shi kamar zaki mai ruri, ko beyar mai sanɗa.


Shugabanninku 'yan tawaye ne, abokan ɓarayi, a koyaushe sai karɓar kyautai suke yi, da rashawa. Amma ba su taɓa kare marayu a ɗakin shari'a, ko su kasa kunne ga ƙarar da gwauraye suka kawo ba, wato matan da mazansu suka mutu.


Sojojinsu na ruri kamar zakunan da suka kashe nama, suna kuwa ɗauke da shi don kada wani ya ƙwace musu.


Amma ka sa idonka da zuciyarka ga ƙazamar riba, Da zubar da jinin marar laifi, Da yin zalunci da danniya.


“Annabi da firist, dukansu biyu marasa tsoron Allah ne, Har a cikin Haikalina na tarar da muguntarsu.” Ubangiji ya faɗa.


wato manyan fādawan Yahuza, da na Urushalima, da 'yan majalisa, da firistoci da dukan jama'ar ƙasa, waɗanda suka bi ta tsakanin rababben ɗan maraƙin,


Domin haka zaki daga kurmi zai kashe su, Kyarkeci kuma daga hamada zai hallaka su. Damisa tana yi wa biranensu kwanto, Duk wanda ya fita daga cikinsu sai a yayyage shi, Domin laifofinsu sun yi yawa, Karkacewarsu babba ce.


Ga shi, kowane shugaban Isra'ila da yake cikinka ya himmantu ga zub da jini bisa ga ikonsa.


Kun sa dogararku ga takobi kuna aikata abubuwan bankyama, kowannenku kuma yana zina da matar maƙwabcinsa, da haka za ku iya mallakar ƙasar?” ’


“Dawakansu sun fi damisa sauri, Sun fi kyarketan maraice zafin hali, Sojojin dawakansu suna zuwa a guje. Sojojin dawakansu suna zuwa daga nesa, Sukan tashi kamar gaggafa da sauri don su cinye.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan