Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Zefaniya 2:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Ku nemi Ubangiji, Dukanku masu tawali'u na duniya, Ku waɗanda kuke bin umarninsa. Ku nemi adalci da tawali'u. Watakila za a ɓoye ku a ranar hasalar Ubangiji.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 Ku nemi Ubangiji, dukanku ƙasashe masu tawali’u, ku da kuke yin abin da ya umarta. Ku nemi adalci da tawali’u; mai yiwuwa ku sami mafaka a ranar fushin Ubangiji.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Zefaniya 2:3
44 Iomraidhean Croise  

Ya ce musu, “Tun yaron yana da rai, na yi azumi da kuka, ina cewa wa ya sani, ko Ubangiji zai yi mini jinƙai, ya bar yaron da rai?


Ku je wurin Ubangiji neman taimako, Ku tsaya a gabansa koyaushe.


Ubangiji yana jin daɗin jama'arsa, Yakan girmama mai tawali'u ya sa ya ci nasara.


Matalauta za su ci yadda suke so, Masu zuwa wurin Ubangiji za su yabe shi, Su arzuta har abada!


Ka ɓoye su a wurinka lafiya daga makircin mutane, A inuwa mai lafiya ka ɓoye su daga zargin magabtansu.


Ka yi hawan ɗaukaka zuwa nasara, Domin ka tsare gaskiya da adalci. Saboda ikonka za ka yi babban rinjaye.


Ka yi mini jinƙai, ya Allah, ka yi jinƙai, Gama na zo gare ka neman tsira. Zan sami kāriya a ƙarƙashin fikafikanka, Sai dukan hatsari ya wuce.


Sa'ad da ka tashi domin ka yanke hukunci, Domin ka ceci waɗanda ake zalunta a duniya.


Duk wanda ya je wurin Maɗaukaki Zai zauna lafiya, Duk wanda yake zaune a inuwar Mai Iko Dukka,


Za ku ce, ‘Hadaya ce ta Idin Ƙetarewa ga Ubangiji, domin ya tsallake gidajen Isra'ilawa a Masar, lokacin da ya kashe Masarawa, amma bai taɓa gidajenmu ba’ ” Sai jama'ar suka durƙusa suka yi sujada.


Sunan Ubangiji kamar ƙaƙƙarfar hasumiya ne, inda adali yakan shiga ya zauna lafiya.


Ku koyi yin abin da yake daidai. Ku ga an aikata adalci, ku taimaki waɗanda ake zalunta, ku ba marayu hakkinsu, ku kāre gwauraye, wato matan da mazansu suka mutu.”


Zai yi wa matalauta shari'a daidai. Zai kuma kāre hakkin masu tawali'u. Bisa ga umarninsa za a hukunta ƙasar, Mugaye za su mutu.


Ubangiji ya saukar mini da ikonsa. Ya zaɓe ni, ya aike ni Domin in kawo albishir mai daɗi ga talakawa, In warkar da waɗanda suka karai a zuci, In yi shelar kwance ɗaurarru, Da kuma 'yanci ga waɗanda suke cikin kurkuku.


Gama hakika zan cece ka, ba za ka mutu ta takobi ba. Za ka sami ranka kamar ganimar yaƙi, domin ka dogara gare ni, ni Ubangiji na faɗa.’ ”


Kana nemar wa kanka manyan abubuwa? Kada ka neme su, gama zan kawo masifa a kan dukan 'yan adam, amma zan kuɓutar da ranka kamar ganima, a dukan wuraren da za ka tafi.’ ”


Ba ku ƙaura zuwa inda garu ya tsage ba, ba ku gina wa mutanen Isra'ila garu don su kāre kansu a lokacin yaƙi, a ranar Ubangiji ba.


Ku shuka wa kanku adalci, Ku girbe albarkun ƙauna, Ku yi kautun saurukanku, Gama lokacin neman Ubangiji ya yi, Domin ya zo, ya koya muku adalci.


Girmankan mutanen Isra'ila ya kai ƙararsu, Duk da haka ba wanda ya komo wurin Ubangiji Allahnsu, Ba su kuwa neme shi ba.


Kila Allah zai dakatar da nufinsa, fushinsa ya huce, ya bar mu mu tsira daga mutuwa!”


“Ni Ubangiji Mai Runduna na ce, azumi na watan huɗu, da na watan biyar, da na watan bakwai, da na watan goma, za su zama lokatan murna, da farin ciki, da idodin farin ciki, ga jama'ar Yahuza, saboda haka sai ku ƙaunaci gaskiya da salama.


“Albarka tā tabbata ga masu tawali'u, domin za su gāji duniya.


Daga ƙarshe kuma 'yan'uwa, muna roƙonku, muna kuma yi muku gargaɗi saboda Ubangiji Yesu, cewa kamar yadda kuka koya a wurinmu, irin zaman da ya dace da ku, ku faranta wa Allah rai, kamar yadda yanzu ma kuke yi, to, sai ku ƙara yin haka ƙwarai da gaske,


Hakika kuwa kuna ƙaunar dukan 'yan'uwa a duk ƙasar Makidoniya. Sai dai muna muku gargaɗi, 'yan'uwa, ku ƙara yin haka ƙwarai da gaske,


Da yake kun tsarkake ranku kuna yi wa gaskiya biyayya har kuna nuna sahihiyar ƙauna ga 'yan'uwa, sai ku himmantu ga ƙaunar juna da zuciya ɗaya.


sai dai ya zama na hali, da kuma kyan nan marar dushewa na tawali'u da natsuwa. Wannan kuwa abu ne mai martaba ƙwarai a gun Allah.


Amma ku ƙaru da alherin Ubangijinmu, Mai Cetonmu Yesu Almasihu da kuma saninsa. Ɗaukaka tă tabbata a gare shi a yanzu, da kuma har abada. Amin! Amin!


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan