Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Zefaniya 2:2 - Littafi Mai Tsarki

2 Kafin a zartar da umarni, Kafin a kore ku kamar ƙaiƙayi, Kafin kuma zafin fushin Ubangiji ya auko muku, Kafin ranar hasalar Ubangiji ta auko muku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 kafin ƙayyadadden lokacin nan yă zo ranan nan kuma ta share ku kamar ƙaiƙayi kuma kafin fushi mai tsanani na Ubangiji yă auko muku, kafin ranar fushin Ubangiji ta auko muku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Zefaniya 2:2
22 Iomraidhean Croise  

Ya kuma sa su zama kamar tattakar da iska yake kwashewa? Ko kuma kamar ƙura wadda hadiri yake kwashewa?


Amma mugaye ba haka suke ba, Su kamar yayi suke wanda iska take kwashewa.


Ku yi mubaya'a da Ɗan, Idan kuwa ba haka ba zai yi fushi da ku, za ku kuwa mutu, Gama yakan yi fushi da sauri. Albarka ta tabbata ga dukan masu zuwa gare shi neman mafaka!


“Ku ji wannan ku da kuke ƙyale ni, In ba haka ba zan hallaka ku, Ba wanda zai cece ku.


Al'ummai sun ci gaba kamar sukuwar raƙuman ruwa, amma Allah ya tsauta musu suka kuwa janye, aka kora su kamar ƙura a gefen dutse, kamar kuma tattaka a cikin guguwa.


Ubangiji ba zai huce ba, Sai ya aikata nufin zuciyarsa. Amma sai daga baya za ku gane sarai.”


Ya ku mutanen Yahuza da na Urushalima, Ku yi wa kanku kaciya domin Ubangiji, Ku kawar da loɓar zukatanku Don kada fushina ya fito kamar wuta, Ya cinye, ba mai iya kashewa, Saboda mugayen ayyukan da kuka aikata.”


Ubangiji ya saki fushinsa, Ya zuba fushinsa mai zafi. Ya kunna wa Sihiyona wuta Wadda ta cinye harsashin gininta.


Gama ni Ubangiji zan yi magana, maganata kuwa za ta tabbata, ba za ta yi jinkiri ba, amma za ta tabbata a kwanakinku, ku 'yan tawaye. Zan yi magana, za ta kuwa tabbata, ni Ubangiji Allah, na faɗa.”


Don haka za su zama kamar ƙāsashin da akan yi da safe, Ko kuwa kamar raɓa mai kakkaɓewa da wuri. Za su zama kamar ƙaiƙayi wanda ake shiƙarsa cikin iska a masussuka, Ko kuwa kamar hayaƙin da yake fita ta bututu.


Wa zai iya tsaya wa fushinsa? Wa kuma zai iya daurewa da hasalarsa? Yana zuba hasalarsa mai kama da wuta, Duwatsu sukan farfasu a gabansa.


Azurfarsu da zinariyarsu ba za su cece su A ranar hasalar Ubangiji ba, A cikin zafin kishinsa Dukan duniya za ta hallaka. Zai kawo ƙarshen duniya duka nan da nan.


“Domin haka ni Ubangiji na ce, Ku jira ni zuwa ranar da zan tashi in yi tuhuma. Gama na ƙudura zan tattara al'umman duniya, da mulkoki, Don in kwarara musu hasalata Da zafin fushina, Gama zafin kishina Zai ƙone dukan duniya.


Sararin sama da kasa za su shuɗe, amma maganata ba za ta shuɗe ba.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan