“Ka tattara dukan Yahudawan da suke a Shushan, su yi domin, kada su ci ko su sha dare da rana, har kwana uku. Ni kuma da kuyangina za mu yi haka nan. Sa'an nan zan tafi wurin sarki, ko da yake ba bisa ga doka ba, idan na halaka, na halaka ke nan.”
Sun ji kunya sa'ad da suka aikata abubuwan banƙyama? Ba su ji kunya ba ko kaɗan. Ko gezau ba su yi ba, Don haka za su fāɗi tare da fāɗaɗɗu, Sa'ad da na hukunta su, za a hamɓarar da su. Ni Ubangiji na faɗa.”
Ubangiji wanda yake cikinsa mai adalci ne, Ba ya kuskure. Yakan nuna adalcinsa kowace safiya, Kowace safiya kuwa bai taɓa fāsawa ba. Amma mugu bai san kunya ba.