Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Zefaniya 1:4 - Littafi Mai Tsarki

4 “Zan miƙa hannuna gāba da Yahuza Da dukan mazaunan Urushalima. A wurin nan zan datse saura waɗanda suke bauta wa Ba'al, Da kuma sunayen firistocin gumaka tare da firistocina,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 “Zan miƙa hannuna gāba da Yahuda da kuma dukan mazaunan Urushalima. Zan datse raguwar Ba’al daga wannan wuri, da sunayen firistocin gumaka da na marasa sanin Allah,

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Zefaniya 1:4
14 Iomraidhean Croise  

Zan gwada Urushalima da magwajin Samariya da kuma ma'aunin gidan Ahab. Zan kuma suɗe Urushalima kamar yadda mutum yakan suɗe akushi sa'an nan ya kifar da shi.


Ya rurrushe, ya kuma farfasa bagaden da yake bisa rufin benen Ahaz, waɗanda sarakunan Yahuza suka gina, da kuma bagaden da Manassa ya gina a farfajiya biyu ta Haikalin Ubangiji. Sai ya watsar da tokar da ƙurar a rafin Kidron.


Sai suka farfashe bagadai na Ba'al a gabansa, ya kuma tumɓuke bagadan ƙona turare waɗanda suke a bisansu. Ya ragargaza Ashtarot, da sassaƙaƙƙun siffofi, da na zubi, ya maishe su ƙura. Ya barbaɗa su a kan kaburbura waɗanda suka miƙa hadayu a kansu.


Ka miƙa dantsen damanka, ƙasa ta haɗiye su.


Ni Ubangiji na ce, kun ƙi ni, kuna ta komawa da baya, Don haka na nuna ikona gāba da ku, na hallaka ku, Na gaji da jin tausayinku!


domin haka zan miƙa hannuna gāba da ku, zan bashe ku, ku lalace a ƙasashe, zan hallaka ku. Sa'an nan za ku sani ni ne Ubangiji.”


Zan nuna ikona a dukan ƙasar, in mai da ita da wuraren zamansu duka hamada. Ƙasarsu za ta zama hamada har zuwa Dibla. Kowa zai sani ni ne Ubangiji’ ”


Mazaunan Samariya suna rawar jiki Domin ɗan maraƙin Bet-awen, Mutane za su yi makoki dominsa, Firistoci matsafa, za su yi kururuwa dominsa, Da kuma darajarsa wadda ta rabu da shi.


Zan sassare siffofinku da ginshiƙanku, Ba za ku ƙara sunkuya wa aikin hannuwanku ba.


Ubangiji zai tsananta musu, Zai kawo wa dukan gumakan da yake a duniya yunwa. Kowane mutum a duniya zai yi masa sujada a inda yake, Har da ƙasar sauran al'umma.


Zai miƙa hannunsa gāba da arewa, Zai hallaka Assuriya, Zai mai da Nineba busasshen kufai Marar amfani kamar hamada.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan