Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Zefaniya 1:3 - Littafi Mai Tsarki

3 Zan shafe mutum da dabba, Zan shafe tsuntsayen sararin sama da kifayen teku, Zan kuma rushe gumakansu tare da mugaye, Zan kuma datse ɗan adam daga duniya.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

3 “Zan hallaka mutane da dabbobi; zan kuma hallaka tsuntsayen sama da kifayen teku, da gumakan da suke sa mugaye su yi tuntuɓe.” “Sa’ad da zan kawar da mutum daga fuskar duniya,” in ji Ubangiji.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Zefaniya 1:3
22 Iomraidhean Croise  

Sai Ubangiji ya ce, “Zan shafe mutum daga duniya, mutum da dabba, da masu rarrafe, da tsuntsayen sararin sama, gama na damu da na halicce su.”


Ba za a gafarta zunuban Isra'ila ba, sai an niƙe duwatsun bagadan arna su zama kamar alli, har kuma ba sauran keɓaɓɓun ginshiƙai ko bagadan ƙona turare.


Na yi tambaya na ce, “Har yaushe zai ta zama haka, ya Ubangiji?” Sai ya amsa, ya ce, “Har birane suka zama kufai ba kowa ciki. Har gidaje suka zama kangwaye. Har ƙasar kanta ta zama ba kowa, marar amfani.


Zan sa jama'a su tafi nesa, in sa ƙasar duka ta zama kango.


Sai yaushe ƙasar za ta daina makoki, Ciyawar kowace saura kuma ta daina yin yaushi? Saboda muguntar mazaunan ƙasar ne dabbobi da tsuntsaye suka ƙare, Domin mutanen suna cewa, “Ba zai ga ƙarshenmu ba.”


“Wata al'umma za ta taso daga arewa gāba da ita, za ta mai da ƙasar abar ƙyama, ba wanda zai zauna ciki. Mutum da dabba duk sun watse, kowa ya bar ta.”


Saboda haka ga abin da Ubangiji Allah ya ce, “Duba, zan kwarara fushina da hasalata a kan wannan wuri, a kan mutum duk da dabba, da akan itatuwan saura da amfanin gona. Zai yi ta cin wuta, ba kuwa za a kashe ba.”


Zan yi kuka in yi kururuwa saboda tsaunuka, Zan yi kuka saboda wuraren kiwo, Domin sun bushe sun zama marasa amfani. Ba wanda yake bi ta cikinsu. Ba a kuma jin kukan shanu, Tsuntsaye da namomin jeji, sun gudu sun tafi.


Da yake sun hidimta wa mutane a gaban gumakansu, suka zama sanadin mugun tuntuɓe ga mutanen Isra'ila, don haka ni Ubangiji Allah, na yi rantsuwa cewa za su karɓi hakkin muguntarsu.


Sun watsar da azurfarsu a titi, zinariyarsu kuma ta zama kamar ƙazantacciyar aba. Azurfarsu da zinariyarsu ba za su iya cetonsu ba, a ranar fushin Ubangiji. Ba za su iya ƙosar da su ba, gama su ne sanadin tuntuɓensu.


Assuriya ba za ta cece mu ba, Ba kuwa za mu hau dawakai ba. Ba za mu kuma ƙara ce da aikin hannuwanmu, ‘Kai ne Allahnmu,’ ba. A wurinka ne maraya yakan sami jinƙai.”


Ya mutanen Ifraimu, me zan yi da gumaka? Ni ne wanda yake amsa muku, mai lura da ku kuma. Ni kamar itacen fir ne mai ganyaye kore shar. Daga gare ni, kuke samun 'ya'ya.”


Saboda haka ƙasar za ta yi makoki, Dukan waɗanda yake zaune a cikinta za su yi yaushi. Namomin jeji kuma, da tsuntsaye, da kifaye za su ƙare.


A wannan rana fa, ni Ubangiji Mai Runduna, zan shafe sunayen gumaka daga ƙasar, har da ba za a ƙara tunawa da su ba. Zan kuma kawar da annabawa da mugayen aljannu.


Ɗan Mutum zai aiko mala'ikunsa, za su tattaro duk masu sa mutane laifi, da kuma duk masu yin mugun aiki, su fitar da su daga Mulkinsa,


Ina dai gaya muku, ba za ku ƙara ganina ba, sai ran da kuka ce, ‘Albarka ta tabbata ga mai zuwa da sunan Ubangiji.’ ”


Amma ga waɗansu laifofinka kaɗan. Akwai waɗansu a cikinku, da suke bin koyarwar Bal'amu, wanda ya koya wa Balak ya sa Isra'ilawa laifi, don su ci abincin da aka yi wa gumaka sadaka, su kuma yi fasikanci.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan