Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Zefaniya 1:1 - Littafi Mai Tsarki

1 Ubangiji ya yi magana da Zafaniya ɗan Kushi, ɗan Gedaliya, ɗan Amariya, ɗan Hezekiya, a zamanin Yosiya ɗan Amon, Sarkin Yahuza.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Maganar Ubangiji da ta zo wa Zefaniya ɗan Kushi, ɗan Gedaliya, ɗan Amariya, ɗan Hezekiya, a zamanin Yosiya ɗan Amon sarkin Yahuda.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Zefaniya 1:1
12 Iomraidhean Croise  

Manassa ya mutu, aka binne shi a lambun gidansa a gonar Uzza. Ɗansa Amon ya gāji gadon sarautarsa.


Aka binne shi a kabarinsa na gonar Uzza. Ɗansa Yosiya ya gāji sarautarsa.


Haka fa Manassa ya rasu, suka binne shi a gidansa, sai Amon ɗansa ya gāji gadon sarautarsa.


wanda Ubangiji ya yi masa magana a zamanin Yosiya ɗan Amon, Sarkin Yahuza, a shekara ta goma sha uku ta mulkinsa,


Gama haka Ubangiji ya ce a kan Yahowahaz, ɗan Yosiya, Sarkin Yahuza, wanda ya gāji sarautar ubansa, Yosiya, wanda ya tafi ya bar wurin nan. Ba zai ƙara komowa nan ba.


“Shekaru ashirin da uku ke nan tun daga shekara ta goma sha uku ta mulkin Yosiya, ɗan Amon, Sarkin Yahuza, har zuwa yau, Ubangiji ya yi mini magana, ni kuwa na yi ta faɗa muku, amma ba ku ji ba.


Ubangiji ya yi magana da Ezekiyel, firist, ɗan Buzi, a ƙasar Kaldiyawa, kusa da kogin Kebar. Ikon Ubangiji yana bisa kansa.


Ubangiji kuwa ya yi magana da Yusha'u ɗan Beyeri a zamanin mulkin Azariya, da Yotam, da Ahaz, da Hezekiya, sarakunan Yahuza, da zamanin mulkin Yerobowam ɗan Yehowash, Sarkin Isra'ila.


Kowane Nassi hurarre na Allah ne, mai amfani ne kuma wajen koyarwa, da tsawatarwa, da gyaran hali, da kuma tarbiyyar aikin adalci,


Har wa yau kuma, aka ƙara tabbatar mana da maganar annabcin nan, ya kuwa kyautu a gare ku, ku mai da hankali a gare ta, kamar fitila take mai haskakawa a wuri mai duhu har ya zuwa asubahin ranar nan, gamzaki kuma yă bayyana a zukatanku.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan