Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yunana 2:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Na ce, an kore ni daga wurinka, Duk da haka zan sāke ganin Haikalinka mai tsarki.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Sai na ce, ‘An kore ni daga fuskarka; duk da haka zan sāke duba wajen haikalinka mai tsarki.’

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yunana 2:4
20 Iomraidhean Croise  

da manyan al'amura da ka yi wa jama'arka, ya zo domin ya yi maka sujada, da kuma addu'a gare ka a wannan Haikali,


Idan sun komo gare ka da zuciya ɗaya, da dukan ransu a ƙasar abokan gabansu waɗanda suka kai su bauta, suka yi addu'a gare ka, suna fuskantar ƙasarsu wadda ka ba kakanninsu, da birnin da ka zaɓa, da Haikalin da na gina saboda sunanka,


sai in raba jama'ar Isra'ila da ƙasar da na ba su, Haikalin kuma da na tsarkake domin sunana, zan kawar da shi daga gabana. Jama'ar Isra'ila kuwa za su zama abin karin magana, da abin ba'a a wurin dukan mutane.


in sun tuba da zuciya ɗaya, a ƙasar da aka kai su, in sun fuskanci ƙasarsu wadda ka ba kakanninsu, da birnin da ka zaɓa, suka yi addu'a, suna kuma fuskantar Haikalin nan da na gina domin sunanka,


Na ji tsoro, na zaci ka jefar da ni ne daga gabanka. Amma ka ji kukana sa'ad da na yi kira gare ka neman taimako.


Ubangiji ya nuna madawwamiyar ƙaunarsa kowace rana! Ni ma in raira yabo gare shi kowane dare, In yi addu'a ga Allah, wanda ya ba ni rai.


Amma ni, ina iya zuwa wurinka, Saboda ƙaunarka mai girma, In yi sujada a tsattsarkan Haikalinka, In kuma rusuna maka da bangirma.


Ka jefar da ni cikin zurfin kabari, Da cikin rami mafi zurfi, mafi duhu.


Fushinka yana da nauyi a kaina, An turmushe ni a cikin tuƙuƙinka.


Ɓacin zuciyata zai juya ya zama salama. Ka ceci raina daga dukan hatsari, Ka gafarta dukan zunubaina.


Amma mutanen Urushalima suka ce, “Ubangiji ya yashe mu! Ya manta da mu.”


Sai Ubangiji ya ce mini, “Ko da a ce Musa da Sama'ila za su tsaya a gabana, duk da haka zuciyata ba za ta komo wurin mutanen nan ba. Ka kore su daga gabana su yi tafiyarsu!


Zan kore ku daga gabana kamar yadda na yi wa dukan 'yan'uwanku, dukan zuriyar Ifraimu.’ ”


Ruwa ya sha kaina, Sai na ce, ‘Na halaka.’


Sa'an nan Ubangiji ya ce mini, “Ɗan mutum waɗannan ƙasusuwa su ne mutanen Isra'ila duka. Ga shi, suna cewa, ‘Ƙasusuwa sun bushe, zuciyarmu kuwa ta karai, an share mu ƙaƙaf.’


Sa'ad da Daniyel ya sani an sa hannu a dokar, sai ya tafi gidansa. Ya buɗe tagogin benensa waɗanda suke fuskantar Urushalima. Sau uku kowace rana yakan durƙusa ya yi addu'a, yana gode wa Allahnsa kamar yadda ya saba.


Sa'ad da na ji raina yana rabuwa da ni, Sai na tuna da kai, ya Ubangiji. Addu'ata kuwa ta kai gare ka a Haikalinka tsattsarka.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan