Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yunana 2:2 - Littafi Mai Tsarki

2 ya ce, “A cikin wahalata na yi kira gare ka, ya Ubangiji, Ka a kuwa amsa mini. Daga can cikin lahira na yi kira, Ka kuwa ji muryata.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 Ya ce, “A cikin damuwata na yi kira ga Ubangiji, ya kuwa amsa mini. Daga cikin zurfi kabari na yi kiran neman taimako, ka kuwa saurari kukata.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yunana 2:2
26 Iomraidhean Croise  

Amma sa'ad da yake wahala, sai ya roƙi jinƙan Ubangiji Allahnsa, ya ƙasƙantar da kansa sosai a gaban Allah na kakanninsa.


Mutuwa ta ɗaure ni da igiyarta tam, Razanar kabari ta auka mini, Na cika da tsoro da alhini.


Sa'ad da nake shan wahala, Na yi kira ga Ubangiji, Ya kuwa amsa mini.


Saboda ba za ka yarda in shiga lahira ba, Ba za ka bar wanda kake ƙauna a zurfafa daga ƙarƙas ba.


Ba ya ƙyale matalauta, Ko ya ƙi kulawa da wahalarsu, Ba ya rabuwa da su, Amma yakan amsa lokacin da suka nemi taimako.”


Marasa galihu suka yi kira gare shi, ya kuwa amsa. Ya cece su daga dukan wahalarsu.


Ka amsa mini sa'ad da na yi kira, Ya Allah, madogarata! Lokacin da nake shan wahala, ka zama mai taimakona. Ka yi mini alheri, ka kuma saurari addu'ata!


Sa'ad da nake nesa da gida, zuciyata ta karai, Zan yi kira gare ka! Ka kai ni lafiyayyiyar mafaka.


Saboda kakan amsa addu'o'i, Dukan mutane za su zo wurinka.


Wane irin girma madawwamiyar ƙaunarka take da shi a gare ni! Gama ka cece ni daga zurfin kabari.


“Lahira tana shirye-shiryen yi wa Sarkin Babila maraba. Fatalwan waɗanda suka yi iko a duniya suna kaiwa suna komowa a hargitse. Fatalwan sarakuna suna tashi daga gadajen sarautarsu.


“Ya Ubangiji, na yi kira ga sunanka Daga cikin rami mai zurfi.


sa'an nan zan tura ki tare da waɗanda suke gangarawa zuwa lahira, zuwa wurin mutanen dā. Zan sa ki zauna a ƙarƙashin ƙasa inda ya zama kufai, tare da waɗanda suke gangarawa zuwa lahira, don kada a zauna a cikinki, amma zan ƙawata ƙasar masu rai.


An yi wannan domin kada itatuwan da suke bakin ruwa su yi girma, su yi tsayi da yawa har kawunansu su kai cikin gizagizai, domin kuma kada itacen da yake shan ruwa ya yi tsayi kamarsa, gama an bashe su ga mutuwa zuwa lahira, tare da 'yan adam masu gangarawa zuwa cikin kabari.”


Wato, kamar yadda Yunusa ya yi kwana uku dare da rana cikin wani babban kifi, haka kuma Ɗan Mutum zai yi kwana uku dare da rana a cikin ƙasa.


Duk wanda ya roƙa, akan ba shi, mai nema yana tare da samu, wanda ya ƙwanƙwasa kuma za a buɗe masa.


Domin kuma yana shan wahala gaya, sai ya ƙara himmar addu'a, har jiɓinsa yana ɗiɗɗiga ƙasa kamar manyan ɗarsashin jini.]


Domin ba za ka yar da raina a Hades ba, Ba kuwa za ka yarda Mai Tsarkinka ya ruɓa ba.


Almasihu, a lokacin zamansa a duniya, ya yi addu'o'i da roƙe-roƙe, tare da kuka mai tsanani, har da hawaye, ga wannan da yake da ikon cetonsa daga mutuwa, aka kuwa saurare shi saboda tsananin miƙa kansa.


Kada ka zaci ni 'yar iska ce. Ni dai ina faɗar damuwata da tsokanar da ake yi mini ne.”


Dawuda kuwa ya damu ƙwarai gama mutane suna niyyar su jajjefe shi da duwatsu, domin ransu ya ɓace saboda 'ya'yansu mata da maza. Amma Ubangiji Allahnsa ya ƙarfafa shi.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan