Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yunana 1:4 - Littafi Mai Tsarki

4 Amma Ubangiji ya aika da iska mai ƙarfi a tekun, hadirin ya tsananta ƙwarai har jirgin yana bakin farfashewa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

4 Sai Ubangiji ya aika da babban iska a bisan teku, hadiri ya tsananta ƙwarai har jirgin ya yi barazanar farfashewa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yunana 1:4
13 Iomraidhean Croise  

Yana aikata dukan abin da ya ga dama a Sama ko a duniya, A tekuna, da kuma zurfafan da suke ƙarƙas.


Yakan kawo gizagizan hadiri daga bangayen duniya, Yakan yi walƙiya domin hadura, Yakan fito da iska daga cikin taskarsa.


Ku yabe shi, ku walƙiya, da ƙanƙara, da dusar ƙanƙara, Da gizagizai, da ƙarfafan iska waɗanda suke biyayya da umarnansa!


Sai Musa ya miƙa sandansa bisa ƙasar Masar, Ubangiji kuwa ya sa iskar gabas ta hura a ƙasar dukan yini da dukan dare, har safiya. Iskar gabas ɗin kuwa ta kawo farar.


Ubangiji kuwa ya sa iska mai ƙarfi ta huro daga wajen yamma, ta kwashi farar, ta zuba ta a Bahar Maliya. Ko fara guda ba ta ragu a cikin iyakar Masar ba.


Da Musa ya miƙa hannunsa bisa bahar, sai Ubangiji ya sa iskar gabas mai ƙarfi ta tsaga bahar, ta tura ta baya, ta yi ta hurawa dukan dare har bahar ta bushe, ruwan kuwa ya dāre.


Ka hura iskarka, bahar ta rufe su, suka nutse kamar darma cikin manyan ruwaye.


Bisa ga umarninsa ruwan da yake samaniya yakan yi ruri, Yakan sa gajimare su tashi daga ƙarshen duniya, Yakan sa walƙiya ta walƙata cikin ruwan sama, Yakan sa iska ta haura daga cikin taskokinsa.


Allah ne ya yi duwatsu Ya kuma halicci iska. Ya sanar da nufinsa ga mutum, Ya juya rana ta zama dare. Yana sarautar duniya duka. Sunansa kuwa Ubangiji Maɗaukaki!


Sai iska ta huro daga wurin Ubangiji, ta koro makware daga teku, ta bar su birjik kusa da zango, misalin nisan tafiyar yini guda ta kowace fuska. Tsayin tashinsu daga ƙasa misalin kamu biyu ne.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan