Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yunana 1:2 - Littafi Mai Tsarki

2 “Ka tashi ka tafi Nineba, babban birnin nan, ka faɗakar da su, gama na ga irin muguntarsu.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

2 “Tafi babban birnin nan Ninebe ka yi mata wa’azi, saboda muguntarta ta haura zuwa gabana.”

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yunana 1:2
24 Iomraidhean Croise  

Daga wannan ƙasa ya tafi Assuriya ya gina Nineba da Rehobot-ir, da Kala,


Sennakerib Sarkin Assuriya, kuwa ya tashi, ya koma gida, ya zauna a Nineba.


Amma wani annabin Ubangiji yana nan, sunansa Oded. Shi wannan annabi ya tafi ya taryi rundunar da ta zo Samariya, ya ce musu, “Ga shi, saboda Ubangiji Allah na kakanninku ya yi fushi da Yahuza, ya bashe su a hannunku, ku kuka kashe su da zafin fushi wanda ya kai har sama.


Na ce, “Ya Allahna, kunya ta rufe fuskata, ban iya in ko ɗaga idanuna wajenka ba, gama muguntarmu ta sha kanmu, tsibin zunubanmu kuma ya kai har sammai.


Sa'an nan sai Sarkin Assuriya, wato Sennakerib, ya janye ya koma Nineba.


Ubangiji ya ce, “Ku yi kuka da ƙarfi, ba ƙaƙƙautawa! Ku ta da muryoyinku kamar busar ƙaho. Ku shaida wa jama'ata laifinsu, ku shaida wa zuriyar Yakubu zunubansu.


Idan na ce, ‘Ba zan ambaci Ubangiji ba, Ban zan ƙara yin magana da sunansa ba,’ Sai in ji damuwa a zuciyata, An kulle ta a ƙasusuwana, Na gaji da danne ta a cikina, Ba zan iya jurewa ba.


Za ka faɗa musu maganata, ko su ji, ko kada su ji, gama su 'yan tawaye ne.


Amma ba su tunani, Cewa zan tuna da dukan muguntarsu. Yanzu ayyukansu sun kewaye su, Ina ganinsu.


“Ka tashi ka tafi Nineba, babban birnin nan, ka yi musu shelar saƙon da zan faɗa maka.”


Sai Yunusa ya tashi ya tafi Nineba kamar yadda Ubangiji ya faɗa masa. Nineba kuwa babban birni ne. Zai kai mutum tafiyar kwana uku kafin yă ƙure birnin.


Ashe, dole ne ni kuma in ji tausayin Nineba, babban birni mai 'yan yara fiye da dubu ɗari da dubu ashirin marasa alhaki, da kuma dabbobi masu yawa.”


Amma ni ina cike da iko, Da Ruhun Ubangiji, Da shari'a da ƙarfin hali, Don in sanar wa Yakubu da laifinsa, Isra'ila kuma da zunubinsa.


Jawabi a kan Nineba ke nan, a littafin wahayin Nahum na Elkosh.


Ba abin da zai rage zafin rauninka, Rauninka ba ya warkuwa. Duk wanda ya ji labarinka, zai tafa hannuwansa Gama wane ne ba ka musguna wa ba?


Za su kuma ja ku gaban mahukunta da sarakuna saboda ni, domin ku ba da shaida a gabansu, a gaban al'ummai kuma.


A Ranar Shari'a mutanen Nineba za su tashi tare da mutanen zamanin nan, su kā da su, don sun tuba saboda wa'azin Yunusa. Ga kuma wanda ya fi Yunusa a nan.


Ga shi kuwa, zaluncin da kuka yi na hakkin masu girbi a gonakinku yana ta ƙara, kukan masu girbin kuwa ya kai ga kunnen Ubangijin Runduna.


Domin zunubanta sun yi tsororuwa, sun kai har Sama, Allah kuwa ya tuna da laifofinta.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan