Aka ƙware shi ba tausayi, Amma ya karɓa da tawali'u, Bai ko ce uffan ba. Kamar ɗan rago wanda ake shirin yankawa, Kamar tunkiya wadda ake shirin yi wa sausaya, Bai ko ce uffan ba.
A cikin annabawa wane ne kakanninku ba su tsananta wa ba? Sun kuma kashe waɗanda suka yi faɗi a kan zuwan Mai Adalcin nan, wanda a yanzu kuka zama maciya amanarsa, da kuma makasansa,
Wannan kuwa shi ne nassin da yake karantawa, “An ja shi kamar tunkiya zuwa mayanka. Kamar yadda ɗan rago yake shiru a hannun mai sausayarsa, Haka, ko bakinsa bai buɗe ba.