Masu ba da rance da ruwa suna zaluntar jama'ata, masu ba da bashi kuwa suna cutarsu. Ya jama'ata, shugabanninku a karkace suke bi da ku, saboda haka ba ku san inda za ku nufa ba.
“Zan nemo ɓatattu, in komo da waɗanda suka yi makuwa, in ɗora karyayyu, in ƙarfafa marasa ƙarfi, amma zan hallaka ƙarfafan makiyayan nan masu taiɓa, zan hukunta su.
Ba ku ƙarfafa marasa ƙarfi ba, ba ku warkar da marasa lafiya ba, ba ku ɗora karayyu ba, waɗanda kuma suka yi makuwa ba ku komar da su ba, waɗanda suka ɓace ba ku nemo su ba, amma kuka mallake su ƙarfi da yaji.
Ya ku 'yan'uwa, in an kama mutum yana a cikin yin laifi, ku da kuke na ruhu, sai ku komo da shi a kan hanya da tawali'u, kowa yana kula da kansa kada shi ma ya burmu.
Ai, son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Don tsananin jarabar kuɗi kuwa waɗansu mutane, har sun bauɗe wa bangaskiya, sun jawo wa kansu baƙin ciki iri iri masu sukar rai.
to, yă dai tabbata, kowa ya komo da mai zunubi a hanya daga bauɗewarsa, ya kuɓutar da ran mai zunubin nan ke nan daga mutuwa, ya kuma rufe ɗumbun zunubansa.