Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 5:17 - Littafi Mai Tsarki

17 Iliya ɗan adam ne kamarmu, amma da ya nace da addu'a kada a yi ruwa, sai da aka shekara uku da wata shida ba a yi ruwa a ƙasar ba.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

17 Iliya mutum ne kamar mu. Ya yi addu’a da gaske don kada a yi ruwan sama, ba a kuma yi ruwan sama a ƙasar ba har shekaru uku da rabi.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 5:17
7 Iomraidhean Croise  

Wani annabi mai suna Iliya, mutumin Tishbi a Gileyad, ya ce wa sarki Ahab, “Na rantse da Ubangiji, Allah na Isra'ila, wanda nake bauta wa, ba za a yi raɓa ko ruwan sama cikin shekarun nan ba, sai da faɗata.”


Bayan 'yan kwanaki, sai Ubangiji ya yi magana da Iliya a shekara ta uku, ya ce, “Tafi, ka nuna kanka ga Ahab, ni kuwa zan sa a yi ruwan sama.”


Amma gaskiya nake gaya muku, a zamanin Iliya akwai mata gwauraye da yawa a Isra'ila, wato a lokacin da aka hana ruwan sama har shekara uku da wata shida, sa'ad da babbar yunwa ta game dukan ƙasar.


Amma Bitrus ya tashe shi, ya ce, “Tashi, ai, ni ma ɗan adam ne.”


“Don me kuke haka? Ai, mu ma 'yan adam ne kamarku, mun dai kawo muku bishara ne, domin ku juya wa abubuwan banzan nan baya, ku juyo ga Allah Rayayye, wanda ya halicci sama, da ƙasa, teku, da kuma dukkan abin da yake a cikinsu.


Ko kaɗan, Allah bai juya wa jama'arsa da ya zaɓa tun dā baya ba. Ko ba ku san abin da Nassi ya faɗa ba ne, a game da Iliya? Yadda ya kai kuka ga Allah, a kan Isra'ila, ya ce,


Suna da ikon hana ruwan sama, don kada a yi ruwa a duk kwanakin da suke yin annabci, suna kuma da iko a kan ruwa, su mai da shi jini, su kuma ɗora wa duniya kowane irin bala'i, a duk lokacin da suke so.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan