Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 5:16 - Littafi Mai Tsarki

16 Saboda haka, sai ku riƙa bayyana wa juna laifofinku, kuna yi wa juna addu'a, don a warkar da ku. Addu'ar mai adalci tana da ƙarfin aiki ƙwarai da gaske.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

16 Saboda haka, ku furta wa juna zunubanku, ku yi addu’a saboda juna, domin ku sami warkarwa. Addu’ar mai adalci tana da iko da kuma amfani.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 5:16
68 Iomraidhean Croise  

Amma sa'ad da Allah ya hallaka biranen kwarin, ya tuna da Ibrahim, ya fid da Lutu daga halakar.


Ibrahim ya yi addu'a ga Allah, Allah kuwa ya warkar da Abimelek, da matarsa, da bayinsa mata, har kuma suka sami haihuwa.


Yanzu fa, sai ka mayar wa mutumin da matarsa, gama shi annabi ne, zai yi maka addu'a, za ka kuwa rayu. In kuwa ba ka mayar da ita ba, ka sani hakika za ka mutu, kai, da dukan abin da yake naka.”


Sai ya ce, “Ba za a ƙara kiranka da suna Yakubu ba, amma za a kira ka Isra'ila, gama ka yi kokawa da Allah da mutane, ka kuwa yi rinjaye.”


Ya ce wa sarki, “Ina roƙon Ubangijina, sarki, in ka yarda kada ka riƙe baranka da laifi, kada ka tuna da laifin da baranka ya yi a ranar da Ubangijina sarki yake gudu daga Urushalima. Kada sarki ya riƙe wannan a zuci.


Sarki Yerobowam ya ce wa annabin, “In ka yarda ka yi roƙo ga Ubangiji Allahnka domina, ka yi mini addu'a don ya warkar da hannuna.” Annabi ya roƙi Ubangiji, sai hannun sarki ya komo daidai.


Ubangiji kuwa ya ji Hezekiya, ya warkar da jama'ar.


Yanzu fa, sai ku kama bijimai bakwai da raguna bakwai, ku kai wa Ayuba, ku miƙa su hadaya ta ƙonawa domin kanku. Ayuba zai yi addu'a dominku, ni kuwa zan amsa addu'arsa don kada in sāka muku bisa ga wautarku. Gama ba ku faɗi gaskiya game da ni ba, kamar yadda bawana Ayuba ya yi.”


Ubangiji yana lura da adalai, Yana kasa kunne ga koke-kokensu,


Muddin hannun Musa na miƙe, sai Isra'ilawa su yi ta cin nasara, amma da zarar hannunsa ya sauka, sai Amalekawa su yi ta cin nasara.


Sai Musa ya fita daga wurin Fir'auna ya rabu da birnin. Ya yi addu'a ga Ubangiji sai walƙiya da ƙanƙara suka tsaya, kwararowar ruwa kuma ta ɗauke.


Sa'ad da mutanen kirki sukan yi addu'a, Ubangiji yakan kasa kunne, amma ba ya kulawa da mugaye.


Ubangiji yana murna sa'ad da adalai suke yin addu'a, amma yana ƙin hadayun da mugaye suke miƙa masa.


Idan ka ƙi biyayya ga doka, Allah zai ƙi jin addu'o'inka.


Sai Ubangiji ya ce mini, “Ko da a ce Musa da Sama'ila za su tsaya a gabana, duk da haka zuciyata ba za ta komo wurin mutanen nan ba. Ka kore su daga gabana su yi tafiyarsu!


“Ka kira ni, ni kuwa zan amsa maka, zan kuwa nuna maka manyan al'amura masu girma da banmamaki, waɗanda ba ka sani ba.”


suka ce wa annabi Irmiya, “Muna roƙonka, ka roƙi Ubangiji Allahnka dominmu, dukanmu da muka ragu, gama mu kima muka ragu daga cikin masu yawa, kamar yadda kake ganinmu da idonka.


Sai mutanen suka yi ta yi wa Musa kuka, Musa kuwa ya yi addu'a ga Ubangiji, wutar kuwa ta mutu.


Kome kuka roƙa da addu'a, in dai kuna da bangaskiya, za ku samu.”


yana yi musu baftisma a Kogin Urdun, suna bayyana zunubansu.


Sai duk mutanen ƙasar Yahudiya, da dukan mutanen Urushalima suka yi ta zuwa wurinsa, suna bayyana zunabansu, yana yi musu baftisma a Kogin Urdun.


Sai suka tashi suka zazzaga ƙauyuka suna yin bishara, suna warkarwa a ko'ina.


Mun sani Allah ba ya sauraron masu zunubi, amma duk wanda yake mai bautar Allah, yake kuma aikata nufinsa, Allah yakan saurare shi.


wato labarin Yesu Banazare, yadda Allah ya shafe shi da Ruhu Mai Tsarki da kuma iko, da yadda ya riƙa zagawa na aikin alheri, yana warkar da duk waɗanda Iblis ya matsa wa, domin Allah yana tare da shi.


Da yawa kuma daga cikin waɗanda suka ba da gaskiya suka zo, suna bayyana ayyukansu a fili.


Sai saminu ya amsa ya ce, “Ku roƙar mini Ubangiji kada ko ɗaya daga cikin abin da kuka faɗa ya aukar mini.”


Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Babu wani mai adalci, babu, ko ɗaya,


Kamar yadda masu ɗumbun yawa suka zama masu zunubi ta wurin rashin biyayyar mutum ɗaya, haka kuma ta wurin biyayyar Mutum ɗaya za a mai da masu ɗumbun yawa masu adalci.


Shi ya sa tun a ran da muka ji labarin, ba mu fāsa yi muku addu'a ba, muna roƙo a cika ku da sanin nufin Allah da matuƙar hikima da fahimta na ruhu,


Ku riƙa yin addu'a ba fāsawa.


Allah kansa, mai zartar da salama, yă tsarkake ku sarai, ya kuma kiyaye ruhunku da ranku da jikinku ƙalau, ku kasance marasa abin zargi a ranar komowar Ubangijinmu Yesu Almasihu.


Ya ku 'yan'uwa, ku yi mana addu'a.


Ta wurin bangaskiya Habila ya miƙa wa Allah hadaya mafi kyau a kan Kayinu, ta wurin wannan bangaskiya ce ya kuma sami yardar Allah a kan shi mai adalci ne domin Allah ma ya shaide shi, da ya karɓi abubuwan da ya bayar. Ya mutu kam, amma ta wurin bangaskiyar nan tasa har ya zuwa yanzu yana magana.


Ta wurin bangaskiya Nuhu, da Allah ya yi masa gargaɗi a kan al'amuran da ba a gani ba a lokacin, yana tsoron Allah, ya sassaƙa jirgi, don ceton iyalin gidansa, ta wurin bangaskiya kuma ya tabbatar wa duniya laifinta, har ya zama magājin adalcin Allah, wanda yake samuwa ta wurin bangaskiya.


Ku bi miƙaƙƙun hanyoyi ɗoɗar, don kada mai ɗingishi ya gulle, a maimakon ya warke.


Ku yi mana addu'a, gama mun tabbata muna da lamiri mai kyau, muna kuwa so mu tafiyar da al'amuranmu da halin kirki ne.


Sa'an nan Joshuwa ya yi magana da Ubangiji a gaban Isra'ilawa a ranar da Ubangiji ya ba da Amoriyawa gare su, ya ce, “Ke rana, ki tsaya a Gibeyon, Kai kuma wata, ka tsaya a kan kwarin Ayalon.”


Shi kansa ya ɗauke zunubanmu a jikinsa a kan gungume, domin mu yi zamanmu matattu ga zunubi, rayayyu kuma ga adalci. Da raunukansa ne aka warkar da ku.


Mukan kuma sami duk abin da muka roƙa a gare shi, domin muna bin umarninsa, muna kuma yin abin da yake so.


Eli kuwa ya lura da bakin Hannatu sa'ad da take yin addu'a.


Yanzu dai rani ne, ko ba haka ba? Zan roƙi Ubangiji ya aiko da tsawa da ruwan sama, da haka za ku sani, ku kuma ga babbar muguntar da kuka yi wa Ubangiji da kuka roƙa a yi muku sarki.”


Sai Sama'ila ya roƙi Ubangiji, Ubangiji kuwa ya sa aka yi tsawa da ruwan sama a wannan rana. Dukan jama'a kuwa suka ji tsoron Ubangiji da Sama'ila ƙwarai.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan