Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 5:15 - Littafi Mai Tsarki

15 Addu'ar bangaskiya kuwa, za ta warkar da marar lafiya Ubangiji kuma zai tashe shi, in ma ya yi zunubi, za a gafarta masa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

15 Addu’ar da aka yi cikin bangaskiya, za tă warkar da marar lafiya, Ubangiji zai tashe shi. In ya yi zunubi kuwa za a gafarta masa.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 5:15
18 Iomraidhean Croise  

Ba wanda zai zauna a ƙasarmu har ya ƙara yin kukan yana ciwo, za a kuma gafarta dukan zunubai.


Ya ce musu, “Saboda ƙarancin bangaskiyarku. Domin hakika ina gaya muku, da kuna da bangaskiya, ko misalin ƙwayar mustad, da za ku ce wa dutsen nan, ‘Kawu daga nan, ka koma can!’, sai kuwa ya kawu. Ba kuwa abin da zai gagare ku.


Bayan haka Yesu ya same shi a Haikali, ya ce masa, “Ka ga fa, ka warke! To, ka daina yin zunubi, don kada wani abu da ya fi wannan muni ya same ka.”


Nufin wanda ya aiko ni kuwa, shi ne kada in yar da kowa daga cikin dukkan waɗanda ya ba ni, sai dai in tashe su a ranar ƙarshe.


Da yake bisa ga hikimar Allah, duniya ba ta san Allah ta wurin hikimarta ba, sai Allah ya ji daɗin ceton masu ba da gaskiya, ta wurin wautar shelar bishara.


Mun sani shi wannan da ya ta da Ubangiji Yesu daga matattu, mu ma zai tashe mu albarkacin Yesu, yă kuma kawo mu a gabansa tare da ku.


Amma fa sai ya roƙa da bangaskiya, ba tare da shakka ba. Don mai shakka kamar raƙuman ruwan teku yake, waɗanda iska take korawa tana tuttunkuɗawa.


In waninku yana shan wuya, to, sai ya yi addu'a, in kuma waninku yana murna, to, sai ya yi waƙar yabon Allah.


Saboda haka, sai ku riƙa bayyana wa juna laifofinku, kuna yi wa juna addu'a, don a warkar da ku. Addu'ar mai adalci tana da ƙarfin aiki ƙwarai da gaske.


to, yă dai tabbata, kowa ya komo da mai zunubi a hanya daga bauɗewarsa, ya kuɓutar da ran mai zunubin nan ke nan daga mutuwa, ya kuma rufe ɗumbun zunubansa.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan