Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 5:13 - Littafi Mai Tsarki

13 In waninku yana shan wuya, to, sai ya yi addu'a, in kuma waninku yana murna, to, sai ya yi waƙar yabon Allah.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Akwai waninku da yake shan wahala? Ya kamata yă yi addu’a. Akwai wani mai murna? Sai yă rera waƙoƙin yabo.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 5:13
34 Iomraidhean Croise  

Ku raira masa waƙa, ku raira yabo gare shi, Ku faɗi dukan abubuwa masu banmamaki da ya yi!


Sa'an nan ne mutum zai yi addu'a ga Allah, ya karɓe shi, Ya zo gabansa da murna, Allah zai komar wa mutum da adalcinsa.


Ku raira masa waƙa, ku raira yabo gare shi, Ku faɗi dukan abubuwa masu banmamaki da ya yi!


A cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji Ya kuwa amsa mini, ya kuɓutar da ni.


A shan wahalata na kira ga Ubangiji, Na yi kira ga Allahna domin neman taimako. A Haikalinsa ya ji muryata, Kukana na neman taimako ya kai kunnensa.


Ku yi kira gare ni sa'ad da wahala ta zo, Zan cece ku, Ku kuwa za ku yabe ni.”


Sa'ad da suka kira gare ni, zan amsa musu, Zan kasance tare da su sa'ad da suke shan wahala, Zan cece su in girmama su.


Mu zo gabansa da godiya, Mu raira waƙoƙin farin ciki na yabo!


Za su raira waƙa don farin ciki, amma ku za ku yi kuka da karayar zuci.


Da suka bugu da ruwan inabi, sai suka yi yabon gumakansu na zinariya, da na azurfa, da na tagulla, da na baƙin ƙarfe, da na itace, da na dutse.


Mutane sun ce, “Zo, mu koma wurin Ubangiji, Gama shi ne ya yayyaga, Shi ne kuma zai warkar. Shi ne ya yi mana rauni, Shi ne kuma zai ɗaure raunin da maɗauri.


ya ce, “A cikin wahalata na yi kira gare ka, ya Ubangiji, Ka a kuwa amsa mini. Daga can cikin lahira na yi kira, Ka kuwa ji muryata.


Sa'ad da na ji raina yana rabuwa da ni, Sai na tuna da kai, ya Ubangiji. Addu'ata kuwa ta kai gare ka a Haikalinka tsattsarka.


Ko da yake al'ummai suna bin gumakansu, Amma mu za mu bi Ubangiji Allahnmu har abada abadin.


Da suka yi waƙar yabon Allah, sai suka fita suka tafi Dutsen Zaitun.


Domin kuma yana shan wahala gaya, sai ya ƙara himmar addu'a, har jiɓinsa yana ɗiɗɗiga ƙasa kamar manyan ɗarsashin jini.]


Ya kuma ce, “Ya Yesu, ka tuna da ni, sa'ad da ka shiga sarautarka.”


To, ƙaƙa ke nan? Zan yi addu'a da ruhuna, zan kuma yi a game da tunanina. Zan yi waƙar yabon Allah da ruhuna, zan yi a game da tunanina.


To, ƙaƙa abin yake ne, 'yan'uwa? Duk sa'ad da kuka taru, wani yakan yi waƙar yabon Allah, wani kuma koyar da Maganar Allah, wani bayani, wani yin magana da wani harshe, wani kuma fassara. Sai dai a yi kome don ingantawa.


kuna zance da junanku da kalmomin zabura, da waƙoƙin yabo, da waƙoƙi na ruhu, kuna raira waƙoƙi da zabura ga Ubangiji da yabo a zukatanku.


Almasihu, a lokacin zamansa a duniya, ya yi addu'o'i da roƙe-roƙe, tare da kuka mai tsanani, har da hawaye, ga wannan da yake da ikon cetonsa daga mutuwa, aka kuwa saurare shi saboda tsananin miƙa kansa.


A kan misalin shan wuya da haƙuri kuma, 'yan'uwa, ku dubi annabawa ma da suka yi magana da sunan Ubangiji.


Suna raira wata sabuwar waƙa a gaban kursiyin, a gaban rayayyun halittan nan huɗu, da kuma a gaban dattawan nan. Ba mai iya koyon waƙar nan, sai mutum dubu ɗari da dubu arba'in da huɗu ɗin nan, waɗanda aka fanso daga duniya.


suna ta da murya da ƙarfi suna cewa, “Yin ceto ya tabbata ga Allahnmu wanda yake a zaune a kan kursiyin, da kuma Ɗan Rago!”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan