Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 5:1 - Littafi Mai Tsarki

1 To, ina masu arziki? Ku yi ta kuka da kururuwa saboda baƙin ciki iri iri da za su aukar muku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

1 Yanzu fa sai ku saurara, ku masu arziki, ku yi kuka da ihu, saboda azabar da take zuwa a kanku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 5:1
36 Iomraidhean Croise  

Ka cece ni daga gare su da ikonka, Ka cece ni daga waɗanda suke da duk abin da suke so a duniyan nan, Ka hukunta su da wahalar da ka shirya musu, Ka sa har 'ya'yansu, su ma, ta ishe su, Wahalar da ta ragu kuma, ta sami jikokinsu!


Adalai za su arzuta, kamar ganyaye da bazara, amma waɗanda suke dogara ga dukiyarsu za su karkaɗe kamar ganyaye da kaka.


Dukiya ba ta da wani amfani a ranar mutuwa, amma adalci zai hana ka mutuwa.


Ku yi ihu saboda shan azaba, ranar Ubangiji ta yi kusa. Ranar da Mai Iko Dukka zai kawo hallaka.


Mutane a tituna sun sa tsummoki a jikinsu, suka taru a filayen taruwa na birni da a kan rufin ɗakuna, sai makoki suke suna ta kuka.


Domin haka sai ku sa tufafin makoki, Ku yi makoki ku yi kuka, Gama fushin Ubangiji bai rabu da mu ba.”


Ubangiji ya ce, “Kada mai hikima ya yi fariya da hikimarsa, kada mai ƙarfi ya yi fariya da ƙarfinsa, kada kuma mawadaci ya yi fariya da wadatarsa.


Ka ce, ‘Mahaifiyarka zakanya ce a cikin zakoki, Ta yi zamanta tare da 'yan zakoki, Ta yi renon kwiyakwiyanta.


“Ɗan mutum, ka yi annabci, ka ce Ubangiji Allah ya ce maka ka yi kuka, kana cewa, “ ‘Kaito, kaito saboda wannan rana!’


Ya ku manoma, ku yi baƙin ciki, Ku yi kuka, ku da kuke lura da gonakin inabi, Gama alkama, da sha'ir, Da dukan amfanin gonaki sun lalace.


Ya ku firistoci masu miƙa hadayu a bagaden Ubangiji, Ku sa tufafin makoki, ku yi kuka! Ku shiga Haikali, ku kwana, Kuna saye da tufafin makoki, Gama ba hatsi ko ruwan inabi da za a yi hadaya da su, A cikin Haikalin Allahnku.


Ku farka, ku yi ta kuka, ku bugaggu, Ku yi kuka, ku mashayan ruwan inabi, An lalatar da 'ya'yan inabin Da ake yin sabon ruwan inabi da su.


Attajiran birnin sun cika zalunci, Mazaunansa kuwa maƙaryata ne, Harshensu na yaudara ne.


Azurfarsu da zinariyarsu ba za su cece su A ranar hasalar Ubangiji ba, A cikin zafin kishinsa Dukan duniya za ta hallaka. Zai kawo ƙarshen duniya duka nan da nan.


“Yeshurun ya yi ƙiba, yana harbin iska, Ka yi ƙiba, ka yi kauri, ka yi sumul. Ya rabu da Allahn da ya yi shi, Ya raina Dutsen Cetonsa.


In rana ta tāke da ƙunarta, sai ciyawa ta bushe, hudarta ta kaɗe, kyanta kuma ya gushe. Haka ma mai arziki zai gushe yana a cikin tsakiyar harkarsa.


Amma, kun wulakanta matalauta! Ashe, ba masu arzikin ne suke matsa muku ba? Ba su ne kuwa suke janku zuwa gaban shari'a ba?


To, ina masu cewa, “Yau ko gobe za mu je gari kaza, mu shekara a can, mu yi ta ciniki, mu ci riba”?


Ku yi nadama, ku yi baƙin ciki, ku yi ta kuka. Dariyarku tă zama baƙin ciki, murnarku tă koma ɓacin zuciya.


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan