Biblia Todo Logo
Bìoball air-loidhne

- Sanasan -




Yaƙub 4:7 - Littafi Mai Tsarki

7 Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah, ku yi tsayayya da Iblis, lalle kuwa zai guje muku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac

Sabon Rai Don Kowa 2020

7 Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah. Ku yi tsayayya da Iblis, zai kuwa guje ku.

Faic an caibideil Dèan lethbhreac




Yaƙub 4:7
32 Iomraidhean Croise  

Amma idan Ubangiji bai ji daɗina ba, to, ga ni, sai ya yi yadda ya ga dama da ni.”


Kada ku yi taurin kai kamar yadda kakanninku suka yi, amma ku miƙa kanku ga Ubangiji, ku zo Wuri Mai Tsarki, wanda ya tsarkake har abada, ku bauta wa Ubangiji Allahnku, domin ya huce daga zafin fushin da yake yi da ku.


ya ce, “Ban shigo duniya da kome ba, ba kuma zan fita cikinta da kome ba. Ubangiji ya bayar, shi ne kuma ya karɓe, yabo ya tabbata ga sunansa.”


Ku faɗa wa Allah cewa, “Al'amuran da kake aikatawa Suna da banmamaki ƙwarai! Ikonka yana da girma ƙwarai, Har maƙiyanka sukan durƙusa a gabanka don tsoro.


Ka tsauta wa Masar, naman jejin nan Mai zafin hali da yake cikin iwa, Ka tsauta wa sauran al'umma, taron bijiman nan da 'yan maruƙansu, Har dukansu su durƙusa, su miƙa maka azurfarsu. Ka warwatsar da jama'ar nan Masu son yin yaƙi!


Ubangiji ya ce wa Irmiya, “Ka faɗa wa sarki da sarauniya, uwarsa, su sauka daga gadon sarautarsu, Domin an tuɓe kyakkyawan rawanin sarautarsu daga kansu.


Za a kore ka daga cikin mutane zuwa jeji ka zauna tare da namomin jeji. Za ka ci ciyawa kamar sa, za ka jiƙe da raɓa har shekara bakwai cur, sa'an nan za ka sani Maɗaukaki ne yake sarautar 'yan adam, yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama.


Za a kuma kore ka daga cikin mutane zuwa jeji, ka zauna tare da namomin jeji. Za ka ci ciyawa kamar sa har shekara bakwai cur, sa'an nan za ka gane Maɗaukaki ne yake sarautar 'yan adam, yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama.”


Ku shiga bautata, ku kuma koya a gare ni, domin ni mai tawali'u ne, marar girmankai, za ku kuwa sami kwanciyar rai.


“Saboda haka, ya sarki Agaribas, ban ƙi biyayya ga wahayin nan da ya zo mini daga Sama ba.


Amma ka tashi ka shiga gari, can za a faɗa maka abin da za ka yi.”


Don saboda rashin fahimtar hanyar samun adalci, wadda Allah ya tanadar, da kuma neman kafa tāsu hanya, sai suka ƙi bin ita wannan hanya ta samun adalci wadda Allah ya tanadar.


Domin a rubuce yake, “Na rantse da zatina, in ji Ubangiji, kowace gwiwa sai ta rusuna mini, Kowane harshe kuwa sai ya yabi Allah.”


kada kuma ku bar wa Iblis wata ƙofa.


Ku bi juna saboda ganin girman Almasihu.


Saboda haka, sai ku ɗauki dukan makamai na Allah, domin ku iya dagewa a muguwar ranar nan, bayan kuma kun gama kome duka, ku dage.


Har wa yau kuma, ai, muna da ubanninmu na jiki da suke hore mu, mun kuwa yi musu ladabi. Ashe, ba za mu fi yi wa Uban ruhohinmu biyayya ƙwarai ba, mu rayu?


Ku yi biyayya ga kowace hukumar mutane saboda Ubangiji, ko ga sarki, domin shi ne shugaba,


Don haka, sai dai ku ƙasƙantar da kanku ga maɗaukakin ikon Allah, domin ya ɗaukakaku a kan kari.


Sama'ila kuwa ya faɗa masa kome da kome, bai ɓoye masa kome ba. Sai Eli ya ce, “Ai, Ubangiji ne, bari ya yi abin da ya yi masa daidai.”


Lean sinn:

Sanasan


Sanasan